Yana Daga Cikin Bayin Allah wadanda In Suka Fadi Magana Allah Ke Tabbatar dashi..


Inji Mlm Aliyu Wakilin Yan Uwa na Birnin Tudu


Wannan Wani Bangare ne da Firar da Wakilinmu Naziru Sabaty Gusau yayi da Wakilin Yan Uwa na birnin Tudu Mlm aliyu Birnin Tudu A Ziyarar makwancin shaheed ishaq muhammad suleman da Wakilan Ma`asumah sukaje yi a birnin tudu..

MA`ASUMAH: -Kune  tare dashi kundade kuna mu`amala tare dashi kuma a matsayinka na Mai Jagirantar Yan uwa na Wannan gari kozaka iya tuno wasu irin Abubuwa na Alkairi  na wannan  Shaheed ?.

MLm ALIYU: -Alhamdulillah sunana Malam Aliyu Birnin Tudu  kuma nine wakilin yan uwa na garin birnin Tudu karkashin Jagorancin Sayyid Zakzaky  (H).

To Alhamdulillah Akan Shaheed Ishaka
Inada Dan Abinda zan fada akansa saboda nasan dai tun Lokacin daya Tashi Yaro ne mai Nutsuwa  Lokaci guda kuma gashi  Da Tsabar  Biyayya ga duk wani ma,abocin girma yana bashi girmansa  kuma a Lokaci guda duk abinda yace zaiyi indai  Alamari na Addinine to zaiyi shi  bangaren abinda yashafi Infaki kuma duk lokacin da aka bukata yana bayarwa ko baya garinnan zai iya turowa abinda aka bukata akansa,

Alokaci guda kuma Alhamdulillah yana daga cikin bayin Allah wadanda insuka fadi magana Allah (T) yana tabbatar dashi domin ya taba ambatamin ina mai magana nacemai Ishak ya maganan Aure?

 Yace to Wallahi shi Aure banan  kusa gareshi ba Makasudin shi dai wannan Harka Allah yabashi shahada,   Nace to Alhamdulillah muma muna bukatar Haka Ishaka,   kaga wannan Alhamdulillahi na shaideshi akan wannan, kuma bangaren abu (kyauta)  bafa sai ka rokeshi ba,  mudai abinda zamu kara cewa yan uwa na wannan gari muna kara jin dadi game da wannan matsayin da Allah yabashi, illadai kawaidai rashin ganin mutum dai shine kawai muke damuwa akansa amman dai Matsayin da Allah (T) ya dauka ya bashi muma muna burin Allah yakaimu wanan Matsayin, kuma Alhamdulillah muna muku godiya da kuka taso kuka mana wannan jaje Allah Shibiya ku Wakilan Ma`asumah.

MA`ASUMAH: -Akaramakallahu daga karshe wani irin kira zakayi ga Yan,uwa..?

Shawarata ga yan,uwa baki daya Alhamdulillah muna ganin wannan matsayi to matsayi ne Wanda Rago baya samun sa Misali sai antashi tsaye Ankai kololuwa wajen damfaruwa ga Allah,  Kusanci ga Allah shi ne Sirrin,  ko yaushe Jagoran wannan Harka keyimana bayani akan mu kusanci Allah,  to kaga yakamata ace wandanna abubuwan sun zamo jiki garemu musani matsayin shahada wani matsayine Wanda bakowa Allah kebaiwa ba sai Wanda Allah (T) ya zabeshi,  kuma a lokaci guda kuma Allah baiba ragoshi sai Wanda yatashi tsaye akai bazai ba rago ba sai mutun ya mai  kyawawan dabi,u da alaka tsakaninsa da Allah (T) dakuma kyautata alakanka tsakaninka mutane dakuma yawan ibada da karatun Alkur,ani da yawan Adduoi da sauransu wannan dai yana daga cikin Abubuwan da suke iya kai matakin koli na shahada Ina fatan kuma Isha Allahu wannan shine Dan abunda zan  Fada......

MA`ASUMAH: - Mlm Mungode

Muma Mungode da Wannan Ziyarar da kukawowa Dan uwanku.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post