DAGA KHUDUBOBIN IMAM ALI (A.S )
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Cikin khudubobinsa (A.S )yana cewa:
‘’ Wadanda ba sa aikata zunubi kuma an yi musu baiwa da gujewa zunubi, ya kamata su ji tausayin masu aikata zunuban kuma marar sa da'a . Kamata yayi ace sun nutsu a cikin godiya (ga Allah wanda yayi musu wannan baiwa ), kuma ya kamata ta hore su daga neman laifin jama'ah game da mai yi da mutane wanda ya dorawa dan'uwansa laifi. Shin , ya sani cewa Allah ya boye laufuffansa da ya aikata , alhalin sun fi na dan'uwan nasa girma?
Yaya za ayi a ce yayi ta zaginsa akan wani zunubi wanda yake shi ma yana aikata irinsa? Ko da bai aikata zunubi irinsa ba lalle ne ya aikata wanda ya fi shi girma. Na rantse da Allah ko da bai aikata manyan zunubai ba, amma ya aikata qanana ne, ai bayyanar da zunuban wasu shi kansa babban zunubi ne.
Yaa ku halittun Allah, kada ku yi gaggawar bayyanar da zunuban wasu , domin kuwa zai iya yiwuwa an gafarta musu (kan zunuban da suka aikata ). Kuma kada ku ji kamar ku kun tsira (daga naku laifuffuksn da kuka aikata )komai qanqantarsu, domin kuwa zai iya yiwuwa a hukunta ku a kansa.
Saboda haka kowa a cikin ku wanda ya san zunubansa wasu kada yace zai bayyana su akan a,inda shi ya sani a game da nasa laifuffukan, kuma kamata ma ya yi yayi ta godiya cewa shi ya tsira ko an tseratar da shi daga abinda wasu suka tsunduma a ciki.‘’
(NAHJUL-BALAGHA , SH:286).
SAI AYI HATTARA 'YAN'UWA !
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
~20th January , 2020.
