Ganin Gazawar `Yan Uwa Ganin Gazawar Allah ne Kan Al`amarin Sayyid (h) ! ! !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @ Shafi domin Kai da Al`ummar ka

ALLAH YA FI KOWA SO DA KISHIN BAYINSA MUMINAI

Muhimmin abu cikin duk abinda dan'uwa zai yi shine, komai nasa ya kasance don Allah yake yin sa. Babban kuskure ne ka ji dan'uwa na zargin kansu ko ganin gazawar wasu kan,al'amarin halin,da jagora Sayyid (H )ke ciki.

Duk wasu matakai na nemawa jagora 'yanci an bi su kuma ana kan bi, Allah shaida ne kuma duniya ma shaida ce kan haka.

Matakan da jagora (H )ya koyar dami kuma ya tafi ya barmi a kansu sune, idan aka danne mana haqqi ko kuma aka ci zarafin wani alami na muslimci , to,,dole ne:-

(a )- Mu fito,kan tituna (Muzaharori )don nuna rashin jin fadinmu ko rashin amincewarmi a aikace.

(b )- Bayyanar da shi wannan abinda aka yi cikin dukkan wasu taruka na wa'azozinmu.

(c )- Bayyanar da shi ta hanyar amfani da manema,labarai.

(d )- Bayyanar da shi ta hanyar rubuce-rubuce a (jaridu ko social media ).

(e )- Addu'o'i kan cewa Allah yayi hukunci kan wannan al'amari .

To, bisa magana ta gaskiya da adalci shine, babu wani dan'uwa ko 'yar'uwa na gaskiya da ba za a sami shi yana aikats daya (1)daga cikin wadannan matakai ba, wasu ma suna aikata uku (3)daga ciki.

Saboda haka banga dalilin da zai sa wani yace gazawar 'yan'uwa bane , ko kuma ya zagi wasu kan cewa babu wani abinda suke yi kan haqqin jagora ba.

Karbar addu'a da zartar da al'amari na hannun Allah ne, kuma shi yace zai taimaki bayinsa muminai. Namu kawai mu motsa ta kowacce fuska.

Allah (T )na cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KU ROQE NI ZAN AMSA MUKU .‘’

‘’ KUMA YA KASANCE HAQQI NE A KANMU TAIMAKON MUMINAI. ‘’

‘’ LALLE NI TARE DA KU INA JI KUMA INA GANI .‘’

Kowa kawai yayi abinda zai iya ba tare da zargin wani ko wasu ba, sai a barwa Allah zartar da al'amarin, domin komai na kasantuwa ne bisa yardarsa (S.W.A ).

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

     08126385470

~20th January , 2020.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Wannan gaskia ne muna fatan Allah ya taimaka mana ya kawo mana karshen wannan jarabawa da gaggawa
    Ilahi

    ReplyDelete
Previous Post Next Post