@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TA HANYAR MURYARTA CE AKE GANE WACECE ITA.
Muslimci addini ne kammalalle wanda ya tattaro duk wani,ilimi,da ya gabata na daga littafan farko, kuma ya tattara duk wani ilimi da fasahar da za ta zo nan gaba. Saboda haka ko da ace za kaga wani abu na cigaban fasaha ya bayyana , to, ba baqon abu ne wanda yazo daga wajen (out of )muslimci ba, a'a, sai dai ace yanzu ne ilimin wannan abu ya bayyana .
Babu wata da'awar muslimci da za ta zo da wani abu wanda za ace su suka gano shi ba, matuqar da ma can yana nan,cikin muslimci , sai dai ace su suka dabbaqa shi sabanin yadda wasu suka gani kuma suka rufe ido ko kawar da kai daga gare shi .
WASU DAGA CIKIN DA'AWOWIN MUSLIMCI
IZALA:- Ana gane wannan da'awa ce ta hanyar furucinsu na cewa babban hadafinsu shine kawai da bidi'a da kuma tsayar da sunnah.
Tabbas, kawai da bidi'ah aiki ne mai girman lada ga wanda yayi, amma kuma tsayar da sunnah zai iya zama tamkar yiwa da'awar Manzo Allah (S.A.W.W )zagon qasa, domin shi (S.A.W.W )kafawa da tabbatar da ita yayi ba tsayar da ita ba, sannan ita sunnah ba ta kafuwa har sai an kawar da kafirci.
GWAGWARMAYAR MUSLIMCI (IMN ):- Ita wannan da'awa ana saurin,fahintarta ne ta hanyar yawaita jin suna kira a dawo kan abinda Manzon Allah (S.A.W.W )ya gina kuma ya barmu a kansa ta hanyar yin riqo da iyalan gidansa (A.S ). Sannan kuma suna kira kan cewa dole ya kasance littafin Allah (T )ne ke jagorantar mu cikin komai namu na rayuwa.
Kuma za ka fahince su ta hanyar furucin su na cewa doke ne a tunbuke mulkin zalunci da azzalumai , domin hakan ne zai bada damar littafin Allah ya kasance shi ke jagorantar mu, amma matuqar su ke jagoranci, to, littafin Allah ba zai taba zama jagora ba.
KUMA TA IRIN WANNAN DA'AWAR CE ANNABI (S.A.W.W )YA BI KUMA YAYI NASARA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~25th January , 2020.
Tags:
Jagoran Gaskiya