Girgizar Kasa Ta Hallaka Mutum 21 A Gabashin Turkiyya

Daga Wakilin Mu --Idishia Jos. Akalla mutum 21 suka mutu, sama da mutum dubu kuma suka samu raunuka sakamakon wata girgizar kasa mai karfi a gabashin Turkiyya. Girgizar kasar mai girman 6.8 ta faru ne a garin Sivrice da ke lardin Elazig inda girgizar kasar ta yi sanadiyar rushewar gine-gine da kuma tursasawa jama’a da dama garari kan tituna. Rahotanni sun bayyana cewa an ji motsi ko kuma karamar girgizar kasa a Syria da Lebanon da kuma Iran da ke makwabtaka da kasar. Tuni dama an saba Tuni dama an saba samun girgizar kasa a Turkiyya inda a shekarar 1999 mutum 17,000 suka mutu a wata girgizar kasa mai karfi da ta faru a garin Izmit da ke yammacin kasar. Girgizar kasar da ta faru a Turkiyya a ranar Juma’a ta faru ne da misalin karfe 17:55 agogon GMT. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post