MARYAM SANDA DA HUKUNCIN BABBAR KOTUN FCT ABUJA: Karin bayani a takaice.
27/1/2020.
Haryanzu Maryam Sanda na da dama na kubuta daga kisa.
By Ishaq Adam Ishaq Esq.
Kasantuwar kotu tayanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa, ba yana nufin za,a aiwatar da hukuncin cikin gaggawa ba ne. Tana iyayin appeal (daukaka kara) zuwa Court of Appeal (kotun da ke gaba da High Court din) a cikin kwanaki 90. Kuma za,a dakatar da aiwatar da hukuncin,harsai kotun ta gama shariar, ta yanke hukunci.
A hukuncin Court of Appeal,idan tayi watsi da hukuncin da FCT High Court ta yanke wa Maryam Sanda na kisa ta hanyar ratayewa, shikenan,sai dai su 'yan sanda ko gwabnati,su daukaka kara. Amma dai za,a sake ta,sai lauyoyinta ne zasuringa zuwa kotu. Idan kuma itama ta tabbatar da wancan hukuncin na FCT High Court, to Maryam Sanda zata daukaka kara zuwa Supreme Court(kotun koli)
Idan kotun koli tayi watsi da hukuncin kisan,shike nan. Idan kuma ta tabbatar dashi, to abisa tsari irin na dokokin Nigeria, ba za,a aiwatar da shi ba. A maimakon haka,a kan canzashi da daurin rai-da-rai ne.
Tun a lokacin mulkin Obasanjo na farar hula,Nigeria ta sanya hannu a bisa wani tsari da kasashen turawa(America, England etc) suka amince da shi na dakatar da aiwatar da kisan kai ga wadan da kotu ta yanke Musu hukuncin kisa(banda irin kamar 'yan fashi da makami)
Abisa wannan tsari,idan kotu kamar High Court tayankewa mutum hukuncin kisa, zai daukaka kara zuwa Court of Appeal. Idan itama ta tabbatar da hukuncin kisan,wanda hakan zaiyi wuya, zai daukaka kara zuwa Supreme Court. Idan itama ta tabbar da hukuncin kisan,wanda da wuya hakan yafaru, to still abisa wancan tsari da Nigeria ta yadda da shi a lokacin Obasanjo,baza,a kashe mutum ba. Sai dai daurin rai-da-rai a gidan kaso.
Sannan tsarin dokokin Nigeria ya yadda da wani abu da ake kira da 'perdon' da 'amnesty' wato yin afuwa ga wanda ko kotu ta yanke masa hukuncin kisa kuma yadade a gidan kaso,ko wanda yayi laifi amma ba,a kamashi ankaishi kotu ba.Gwabna da Shugaban kasa suke da ikon yin perdon ko amnesty(afuwa)
Banbancin Perdon da amnesty shine, perdon sai anyi case din mutum a kotu, anyanke masa hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai. Shi kuwa amnesty ba,akai mutum kotu ba, amma ana tuhumarshi da aikata laifi. Misalin amnesty, kamar lokacin da Umaru Musa 'yar,adu,a ya yiwa 'yan Niger-Delter afuwa. Amnesty kenan. Allah yasa mudace.
Free Allamah Jalaluddeen Sayyid Ibraheem Zakzaky(H)
Via Legal highlight & opinions.
Tags:
Labaran Duniya