Iran zata iya ficewa daga komai saboda kisan Qaseem Sulaimany.
Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Kungiyoyi hudu na kwallon kafa a kasar Iran da ke buga gasar Zakarun Asiya ta AFC Champions League sun ce ba za su buga wasannin gasar ba idan har ba za su karbi bakuncin wasannin ba, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Mehr.
Hukumar kwallon kafar Iran ta ce hukumar AFC ta hana kungiyoyin Iran buga wasanninsu na gida a cikin Iran kuma AFC ta ce ta na son wasannin da kungiyoyin za su yi a buga su a wajen kasar. Wannan yunkurin ya zo ne yayin da dangantaka take kara tsami tsakanin Iran da Amurka tun bayan kisan da sojojin na Amurka suka yiwa babban kwamandan sojojin kasar ta Iran, Qasim Souleimani a farkon wannan watan
Hukumar kula da kwallon kafar Iran ta ce za ta sanar da matsayarta a cikin ‘yan kwanaki “masu zuwa sai dai masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa abune mai wahala Iran din ta amince da bukatar AFC din Iran tana da kungiyoyi hudu a gasar AFC Champions League da suka hada da kungiyar kwallon kafa ta Persepolis da Esteghlal da Sepahan da kuma Shahr Khodro kuma a yau Litinin ake sa ran za a tuntube su.
Sai dai Mehr ya ce kungiyoyin za su mika wasika ga AFC domin bayyana cewa za su fice daga gasar idan ba za su buga wasan gida a Iran ba saboda basu amince suje kowacce kasa ba domin buga wasanninsu na gida.
Saga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya