Gwagwarmayar tumbuke zalumci da shinfida adalci part(1)

"GWAGWARMAYAR TUNBUKE ZALUNCI DA SHINFIDA ADALCI" 1.

🇳🇬
MA, asuma Nigeria news update 🇳🇬
👉by sharhabil Usman pandoss

Akwai bayin Allah suna nan har yanzu a raye tun lokacin Imam na da'awarsa suna samari har yanzu sun tsufa suna nan a raye, basu taba canzawa daga hadafin Imam na gwagwarmaya ba, su ya'yan gwagwarmaya ne, samarin gwagwarmaya ne, dattawan gwagwarmaya ne.

Kullun sautin muryoyinsu na gwagwarmaya ne, da su ake duk fadi tashin kare wannan nizami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tsufansu da girmansu da iliminsu da saninsu bai hanasu tsayuwa kyam wajen kare wannan nizami ba. Kullun maganarsu kasarsu, yan'cin al'ummarsu, kare nizamin Addini da aka tabbatar.

Duk da yake akwai kutsen makiya ta kowane bangare domin su dagula al'amura, wannan bai hana al'ummar kasar tashi tsaye wajen ganin ko da za su rasa rayuwarsu domin kare wannan nizamin sun tabbatar sun cika wannan alkawarin nasu ba, kuma a shirye suke duk inda sayyid Qa'id ya kada su su tunkari wannan wuri da iya karfin sadaukarwarsu.

Shi yunkurin tabbatarda adalci musamman kafuwar nizamin Addini, ba ana tafiya hutun rabin lokaci bane, ana tafiya ne kai tsaye ba dare ba rana, idan ka tafi hutun rabin lokaci makiya za su iya amfani da wannan damar su kamfaci Imaninka ka sani ko baka sani ba. A wannan yanayi da muke ciki ba babba ba yaro, da mai ilmi da almajiri duk aiki guda ne ya rataya a wuyayanmu, kuma gorgodon gudumuwarda dan'uwa zai bayar gorgodon darajarsa da matsayinsa a wajen Allah (T). 

Ba kamar yadda muke ganin wasu abubuwa bane, kamar misalin a nuna wasu ko wani a karatu, ko a iya malkwaya magana, ko sani ace shine ko su ne sukafi kowa ba, sam ba haka bane, aiki ne. Gwagwarmaya musamman a wannan yanayi da muke a ciki, dole ne ya zama da gangan jikinka da ruhinka da zuciyarka da dukiyarka da hikima da karatu da duk baiwarda Allah ya yi maka ka kasance cewa kana tareda ma'abota gwarmaya, ba za kayi wani abu ka ki wani abu ba, ko ka soke shi, ko ka yi masa zagon kasa sannan kuma ka maida wannan abin shine gwagwarmaya, lallai idan da muna kula da matsaya da su Jagoranmu suka dauka tun bayan faruwar wannan waki'ar zuwa yau, da mun tsallake wasu gadoji da dama wadanda makiya suka gitta mana, Allah (T) ya amfanar da mu.


— 19/01/2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post