Idan Su (Azzalumai) Sun Manta To, Mu Tuna Masu Malam (H) Nada Mabiya!!!


Idan Ba Malam (H), Kowa Tashi Taa Zo.

🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update

Daga Wakilinmu
➝MJ Matashi Ibrahim

 Cikin Jawabin Malam Muhammad Maina

To, dan abunda na manta (ban magana ba a farkon jawabi na), shi ne halin da muke ciki. Na san da yawa ba baqon abu ba ne kowa ya san a ina Malam (H) ya ke yanzu; a gidan yari ya ke, kowa ya san su Malam (H) ba su da lafiya. Kowa ya san da suratan da Gwamnatin Kaduna ta yi.. To kuma ban tunanin akwai wanda yake da shakka qudurin su (Azzaman) kamar yadda Malam (H) ya fada a wani 'audio', lokacin su na Abuja cewa me su ke son su yi? Kisa su ke so su yi!

To dole ya zama cewa a matakin farko, kamar yanda na fada cewa duk ni'imonin da Allah ta'ala Ya Yi mana (na addini), ba mu iya ganewa ba sai domin su Malam (H), kuma Malam (H) yana da haqqi a kanmu. Rahamar rayuwar mu da kyautatuwanta a duniya da lahira, ta danfaru ne da su Malam (H). Lahirar; da su Malam (H), kyautatuwanta a nan duniya kuwa, kun san addini ba ya zo kawai ya gyara lahirar mutum ba ne; ya zo ya gyara har duniyar ne.

To gyaruwan ta a nan duniyar, wallahi tallahi tana danfare da rayuwar su Malam (H). Wannan qarnin da muke ciki, samun mafita a wannan nahiyar da wannan qasar; a'a ba wai mu kadai ba (yan uwa), da duk wanda ma yake qasar, a ce watarana qasar za ta zama lafiya daidai, mutum zai rayu kamar rayuwar Dan Adam ba rayuwar dabbobi ba, to ta danfaru ne da rayuwar su Malam (H). Yau aka ce ba Malam (H), kowa ta shi ta zo! Sai 'yan Afghanistan sun mana kuka, sai mutanen Yemen sun dinga jin tausayinmu, sai mutanen Syria da Libya sun dinga lahaula wala quwati su na kuka idan an hasko Najeriya. Ai kowa ya san me ke faruwa a wadannan qasashen ko? To sai sun tausaya mana idan ba rayuwar su Malam (H).

Ko da baka san lahira ba, baka gane wancan haqqin na Allah da Annabi ba, to malam yana da haqqin rayuwar duniyar ka ta kyautatu. In aka ce rayuwar duniyar ka ta kyautatu ba dole ya zama lokacin ka ba, ai mutum ya damu da rayuwar 'yayansa da jikokinsa, ko kai za ka iya sadaukarwa domin su su zo su ji dadi. To ko domin hakan, ya kamata mu tashi domin nema wa su Malam (H) yanci.

Kamar yanda muka fada, ba wani abu da yake samuwa da addu'a ko zikiri kadai, dole ne sai an hada da aiki tare da tawakkali. Aikin nan kuma a fili yake kowa ya san meye aikin; mu fita qwammu da kwarkwatarmu mu nuna ba mu yarda da wannan zaluncin ba. Wannan sassauqan abu ne. Ba a ma je ga cewa "kutiba alaikuml qilatu ba". Wannan fita ne kawai za ka yi ka ta yin slogan. Watakila a ce za a zo kama ka, a raunata, dauri ko kisa.

To a babin godewa Allah bisa ni'imonin sa ma, to baka qure maleji ba ( ko da dayan ukun ya same ka). Ko kashe ka aka yi, wanda ita ce cikakkiyar godiyar, to a hakama Allah kuma Allah Ya yi ma tagomashi ne na sakayya da shahada bisa godiyarka.

To daman dai banso a ce na gama ban yi magana a kan halin da ake ciki ba, ko ba komai an kusa komawa kotu, kotun da a nan su ke tunanin yin duk abunda za su yi. To, akwai bukatar tsaurara addu'oi. Munsan muhimmnacin tawakkali da addu'a. Ana buqatar ta da gasken gaske! Haka kuma, ana bukatar tsaurara fita muzaharori a ko'ina; qauyuka ne, garuruwa da kuma ina? Abuja, inda nan ne suka fi jin zafin ta.

Ya zama aqalla kafin wannan lokacin (komawa kotu), in sun manta ne mu tuna ma su cewa Malam yana da mabiya, mabiyan da ya fada ya ce ba za a iya kashe mutum mai tarin mabiya ma su sadaukarwa, sannan wanda ya yi kisan ya dauka zai je ya ci gaba da rayuwanshi lafiya! Kamar sun manta ne, to ya kamata mu fito mu tuna ma su da cewa fa akwai wadannan mutanen, da idan wani abu ya sami su Malam na qudurin da su ke nufin yi, to ko shelantawa su ka yi, to su san cewa qasar ba kuma yanda su ka santa ba ne, wani abu ne daban zai canza! Sai dai wata Najeriyar da ba wannan ba aqalla su san akwai wannan!

Ba ina nufin taba wanda ba su ji ba su gani ba, Saboda dama sun samar da kayan wasan su Boko Haram, wato ma su zuwa kasuwa su yi hayaniya, ko masallatai da makarantu. To ba ko daya. Dan canza qasar nan, ba ka bukatar sai ka je kasuwa ka dami mutanen kasuwa, ka dami mutanen massalaci ko makaranta. Ba ko daya.

Akwai asalin azzaluman, wanda ba su cika tirelar mota daya ba, da ka tattare su kai maganin su to shikenan, qasar za ta dawo daidai, to su mu ke nufi. Su wadannan yan iskan azzaluman da su ka yamutsa Kasar, su ka sayar da mutuncin qasar da komai, su ke shan jinin mutanen qasar gabadaya ba su yi tirela daya ba. Sauran da ke jikin su duk 'yan ci-ka ba mu ne', karnuka ne kawai.

To su wadancan asalin yan iskan azzaluman, da su mu ke yi, da kuma iyayen gidansu (Amerika da Isra'ila). In wani abu ya samu su Malam (H) to a kan su za ta sauka! Ba Za mu bari a qaryata Malam (H) ba, addu'an mu shi ne Allah Ya yi anfani da mu wurin gasgata su Malam (H).

 Insha Allah. Wasallalhu ala Muhammadin wa alihid dahirin.

Wani yanki kenan daga cikin jawabin Muhammad Maina (Ayatullahi) da ya gabatar a wurin taron Birthday din Shaheed Sayyid Hamid a Gusau, Monday 27 January.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post