Zazzabin lasa:/ MAGANIN CUTAR LASA DAGA MAKARANTAR AHLIL- BAITI (AS)


MAGANIN CUTAR LASA DAGA MAKARANTAR AHLUL BAIT (AS)
.
Shimfida: Ita irin wannan Annoba ce 'Mudlaqa' saboda haka ta barke ne a cikin al-umma kuma tana yaduwa sannan tana kisa saboda haka sunanta Annoba, akwai abubuwa Ma'asurai da akeyi a kubuta daga duk wata Annoba idan ta zo musamman irin wannan Lasa din
.
Duk da ci gaba da ake da shi a duniya da komi da komi amma suna cewa (ita wannan cuta ta Lasa) ba ta da magani sai dai 'Control' kawai, 'Control' din kuma bai wuce shawarwarin yadda za ka kuce ma kamuwa ba, kuma ba lallai ma a sami sakamako dari bisa dari ba wurin kaucewar kuma ko da an 'Dabbaqa' dukkan abinda suke fada suma har yanzu bincike sukeyi babu tabbacin cewa mutum zai iya kubuta din, tunda wataqila sai daga baya su gano abu kaza ma yana daga cikin dalilin kamuwa da cutar, to ka ga wannan matsalace dake bauqatar addu'a, addu'a shine mafi girma kuma kamar yadda nake fada akwai addu'o'i ma'asurai dangane da annoba idan ta shigo cikin al-umma
.
To akwai wadannan ma'asuran Addu'o'i da ayyuka wadanda akeyi domin neman kariya, tunda su ma masana na zamani abinda suke magana a kai shi ne dabarbaru na kariya kawai, *Mu kuma muna da Allah muna da Addu'a kuma  mun san shi yake juya komai*
.
To Insha Allah yanzu akwai wasu abubuwa da za mu kawo wanda suke hana mutum kamuwa da irin wannan annoba, kuma abu ne da yake da muhimmanci dukkanin mumini da yayi imani da Allah da Manzo da Ahlul Bait (As) ya zama ya riqi wannan su zama mashi mafaka, daman Allah da Manzonsa da Ahlul Bait (As) su ne makomar mu kuma su ne mafakan mu mafi qarfi akan dukkannin al-amura, saboda haka za a yi amfani da shawarwarin masana ta wurin kiyayewa da kuma daukan matakan da suke ankararwa wanda idan mutum yabi zai kauce ma wannan to a lokaci guda kuma za'a koma ma Allah ta'ala ta hanyar wadannan ayyuka wadanda suke mafiya qarfi da kuma tasiri saboda haka daman da aiki ne da kuma addu'a haka rayuwa take.
.
*MAGANIN ANNOBA*
.
1. Garkuwa daga Annoba 
.
Yazo cikin littafin Al Maqaal cewa wannan Addu'a ya kamata a rubuta shi a rataya a kofan gida ko daki,  Shi kadai ya isa ya hana 'yan gida ko 'yan dakin kamuwa da Cutar Annoba 👇
*اللهم سكن هيبة صدمة قهرمان الجبروت با اللطيفة النازلة الواردة من فيضان الملكوت. حتي يتشبث بأذيال لطفك عن إنزال قهرك. ويعتصم عن إنزال سخطك. يا ذاالقوة الكاملة والقدرة الشاملة. برحمتك الواسعة. يا رب سكًن سكًن سكًن. يا حي يا محيي الموتي. اللهم يا ولي الأولياء ويا مجيب الدعاء ويا كاشف البلاء. اصرف عنا و عن كل أولادنا واقرباءنا القحط والطاعون والوباء. بحق محمد المصطفى وعلي المرتضى وبحرمة الأيمة والشهداء. وما رميت إذ رميت ولكن الله رمي. وليبلي المؤمنين منه بلاء حسنا. يا غوثاه يا غوثاه يا غوثاه.  اغشنا يا حي يا قيوم يا دائم يا وتر يا ذالجلال والإكرام اللهم خذ ضعفي والطاعون. ومن موة الفجأة. ومن سوء القضاء. ومن درك الشقاء.وشماتة الأعداء. ومن مضرة الحماء . اللهم إني أعوذ بك من جميع ذالك بحق محمد المصطفى وعلي المرتضى والأيمة من ولده النجباء إلهي يا رب العالمين*
.
Kulliyaat Majma'ud da'awat na ibn giyasud deen shafi 38👆
.
2. Kariya daga Annoba 👇
.
*بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وآل محمد بعدد كل داء ودواء يا حفيظ احفظ (wane dan wane) يا لطيف يا حفيظ 
.
Wannan kafa daya ake rubutawa a rike ko a rataya a Matsayin hirzi 

Daga littafin kulliyaat Majma'ud da'awat na ibn giyasud deen shafi 25
.
3. *WARAKA DAGA ANNOBA*
.
*أهيا ادو ها طبوماه صالح همو هم ساهو ماهو استراها ارو بادو ما يويه الها له هالي لوهي امدي هم اسها سربا ها وام ارصغراب هوهو برا ثوره داهيه ادر يوي سمو ممد صالح همه همه إسراهمه لو وربيبو با لوساه* 
.
Ana rubuta wannan a takardu biyu daya asa a Aljihu daya kuma asa A daki ko gida Wato a rataya 
.
Wannan in akayi haka Allah zai kare mutum daga wannan Annoba,  Sannan zai kare gidan da aka rataya wannan 

Daga littafin jaami'ud da'awatil kabeer na ibn giyasud deen shafi 25
.
Shi wannan koda mutum ya kamu ne aka masa zai warke tunda kaga Mu'alaja aka ce,  saboda haka kariya ne kuma Magani ne a lokaci guda 👆
.
4. Kariya daga Annoba
Karanta wannan Addu'a bayan kowace Sallar farillah👇 zai sa mutum ya kubuta daga kamuwa da Annoba
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم إني أسألك الأمن والإيمن بك والتصديك بنبيك والعافية من جميع ألبلاء والشكر على العافية والغنى عن شرار الناس برحمتك يا أرحم الراحيمن (قل من ينجيكم من ظلمت البر ولجر تدعونه تصرعا وخفية لإن أنجنا من هذه لنكونن من الشكرين)
.
Daga littafin Asrarul bayan fi taisiri Ulumir Rahman na Sheikh Bilal Abdul hasan Daha shafi 104
.
5. Kariya daga Annoba
wannan hatimi na cikin wannan hoto👇 Hatimi ne na sunayen A'imma shima na maganin irin wannan annoba, rubuta shi a keyi a nade a riqe.
.

Daga littafin Asrarul bayan fi taisiri Ulumir Rahman na Sheikh Bilal Abdul hasan Daha shafi 104
. DAGA SAYYID ABDULLAHI ASHURA
.
✍ Ammar Abubakar shadow

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post