BREAKING NEWS /gangamin miliyoyi dan korar amerikawa yan mamaya a iraqi a yau juma, a

GANGAMIN MILIYOYI DAN KORAR AMURKAWA YAN MAMAYA, YA FARA A IRAQI YAU JUMA'A.
.
🇳🇬
MA, asuma Nigeria news update 🇳🇬
👉by sharhabil Usman pandoss

Da asubahin Juma'ar yau, al'ummar Iraqi suka fara yin cincirindon zuwa tsakiyar Bagdad, dan amsa kiran malamin addinin nan dan gwagwarmaya, Sayyid Muqtada Sadr, na fitowa su yi gangamin miliyoyi, dan nuna rashin amincewa da cigaba da zaman dakarun mamaya na Amurka a kasarsu.
.
Tun da asubahi masu zanga-zangar ke kwarara zuwa yankin Jadariyya, a tsakiyar Bagdad, dan shiga wannan gangami. Sayyid Muqtada Sadr ne dai ya kirayi magoya bayansa ga yin wannan zanga zanga, ya yin da sauran bangarorin yan gwagwarmaya a Iraqin suka rufa masa baya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post