@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TAGUWAR DA MAFI SHARRIN WANNAN AL'UMMA KE SON KASHE TA.
Babu wani daga cikin Manzanni (A.S )ko kuma mujaddadai da suka yi tajdidin addini ba tare da an cutatar da su ba . Da yawa an kashe su, wasu kuma an cutatar da su kan wannan aiki da Mahaliccinsu (S.W.A )ya dora musu.
Wannan cutarwa ta kasance babbar alama da ke saurin bambance tsakanin wakilan Allah a doron qasa da kuma wakilan shaidan.
Duk wanda kaga irin abinda ya samu Manzanni (A.S )na cutarwa na samunsu, to, wadannan sune magada Annabawan Allah masu aiki irin nasu a doron qasa.
Su kuma wadanda kaga babu abinda ke faruwa da su na cutatarwar zahiri da badini, to, wadannan sune wakilan shaidan a doron qasa.
Tsammani kake aikata addinin gaskiya ne yasa ba a cutatar da kai kan da'awarka?A'a, yin riqo da tafarkin shaidan ne ya ba ka kariya daga cutatawar shaidanu.
Bukhari ya riwaito wani hadisi da zai iya zama hujja kan cewa cutarwa ana yinta ne ga masu riqo ga tafarkin gaskiya .
Ga hadisin kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Umar Bn Hafsin ya bamu labari , babana ya bani labari , A'amashu ya bamu labari yace, wani shaqiqi ya bani labari yace, Abdullahi ya ce:
‘’ Kamar ina gani zuwa ga Annabi (S.A.W.W )da yake bada labarin wani Annabi wanda mutanen sa suka bubbuge shi su kayi masa jina-jina, shi kuma (A.S) yana share jinin daga fuskarsa yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YAA UBANGIJI ! KA GAFARTAWA MUTANENA, DOMIN SU BA SU SANI BANE .‘’
(Bukhari , hadisi me lamba: 6929).
Wato yana nufin mutanen nasa ba su san haqiqanin matsayin sa da kuma amfanin sa gare su bane yasa suke yi masa abinda su kayi.
Kamar dai yadda wannan al'umma ta jahilci matsayin Sayyid (H )da kuma amfanin sa gare su. Shi yasa suke yi masa irin abinda suke yi yanzu a kansa, wasu kuma suna gani hakan daidai ne.
Amma fa bai zama abin mamaki ba don jikokin kafiran Badar suna farin ciki da abinda iyayen su ke yi kan jikokin muminan Badar.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~26th January , 2020.
Tags:
Jagoran Gaskiya