GAREMU MATAN HAUSA FULANI


GAREMU MATAN HAUSA FULANI
M.N.U.030

Ma'asumah Nigeria News Update

Duba da tabarbarewar tarbiyyar zamantakewar aure, musamman ma ga matan hausa Fulani,Zan so nadan tunasar damu wani hadisin manzon Allah (s.a.w.w) Wanda yake cewa: acikin kafi an ruwaito cewa imam Ali (a.s) yace: shi da sayyida Zahara (s.a) sun ziyarci manzon Allah (s) yana kuka ta hanayar zubarda hawaye, bayan sun tambayeshi dadlili sai yace: ya Ali a daren jiya na fita mi'iraji naga wasu Mata daga al'umma ta Wanda ake masu azabobi masu radadi, da tsananin gaske, sai naji tausayinsu na Fara kula.  Yaci gaba dacewa naga wata mace an sarkafeta da nononta.wata kuma tana cin naman jikinta,kuma wuta na fita ta karkashinta, wata kuma an sarkafeta da harshenta, kuma Ana bata tafasasshen ruwan zafi daga makoshinta,wata kuwa an tankwasheta an daure hannuwanta da kakafunta macizai da kunamu duk sun baibaye Mata jiki. Wata Ku ma bebiya kuma makauniya an rufeta a kejin wuta, kwakwalwarta na fita daga ramin gashin kanta,jikinta na yankewa guntu-guntu.
Wata kuma an sarkafeta da kafafunta ta ciki da waje, wata kuma ana yankata da almakashin wuta,wata Mata tanada kan alade da jikin jaki,kuma ana Mata azabobi Kala-Kala,wata kuma tanada fuskar kare wuta na shiga jikinta ta karkashinta tana fita ta bakinta kuma mala'iku na dukanta da rodin karfe.
Sai sayyida Zahara (s.a) ta tambayi babanta tace: yi mana addu'a ka fadamin me wadannan Mata sukayi akemasu haka? Sai manzon Allah (s) yace: ki saurara ya abar kaunata! Ita wadda aka sarkafe da nononta tana hana mijinta damar saduwa da ita, wadda aka sarkafe da kafafuwanta kuwa tana fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba, ita kuwa wadda take cin naman jikinta tanayin kwalliya ta gyara jikinta don ta nunawa mazajen da ba nataba, wadda aka sarkafe kafafuwanta da hannuwanta tare da macizai da kunamu na cinta, bata damu da tsarkake kanta daga najasa ba kuma bata kula dayin wanka yayin daukewar haila da ta bayan jima'i akan lokaci Wanda yana nufin bata damu da ibadarta na.
Ita kuwa bebiya makauniya tana haifar'ya'ya ta hanyar zina amma sai tace na mijintane, wadda ake yanka jikinta da almakashin wuta bata kula da sanya hijabi agaban wanda ba muharraminta ba, wadda ake kona jikinta kuma tana cin hanjin ta to tanakai wasu matan ga mazaje don biyan bukatarsu, ita kuwa mai fuskar kare kuma wuta na shiga ta karkashinta ta fita ta bakinta macece mai bakin kishi. Sai manzon Allah (s) yace: bakin ciki shine sakamakon mai batawa mijinta rai, farin ciki kuma najiran wadda ta sanyashi farin ciki.
Dukkanin wadannan yanayi da manzon Allah (s) ya bayyana mana na wahalhalun da rai zai fuskanta a barzahu kafin tashin kiyama, bala'o'in lahira sunfi zafi da wahala. Abinda ya kamata ma'aurata mu kula dashi anan shine mu kasance masu kyautata zato ga juna, mu zama masu yima juna uziri, sannan mu kasance masu mutunta juna da girmama iyayen juna, sannnan mu kula da hakkokin juna Wanda suke na wajibi, mu kasance masu hakuri domin manzon Allah (s) yace: duk namijin da yayi hakuri kan cutarwar matarsa Allah zai basa lada kamar na annabi yakuba(a.s) sannan duk matar da tayi hakuri kan cutarwar mijinta Allah zai bata lada kamar ta asiya matar fir'auna.

Autar marubuta:- Sakina Ahmad kazaure.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post