DAKE NAKE SISTER

DAKE NAKE SISTER

Ma'asumah Nigeria news update

M.N.U 030

Tare da kanwar ku Sakina Ahmad kazaure.

Zamani ya canja rayuwa muke da wani irin yanayi, duba da yadda wasu daga cikin mu suke mu'amalar su ba wani tsari! Ba kamun Kai, ba girma, sister ki gyara mu'amalarki da al'ummar da kike rayuwa a cikinta. Al'ummar nan zaki iya kasata gida biyu, na farko yan uwa ama da kuma yan uwa khassa.
 Ta janibin mu'amalarki da yan uwa, mu kasance masu girmama juna, nunama junan mu so, tsantsar yan uwantaka, biyayya ga na gaba damu, ba sai iyaye ko yayyen mu ba, ko wane Uba a harkar nan abbanki ne, ko wace Amma ummar kice. A tsakanin mu ya zama akwai kyakkyawar mu'amala kar mu raina kanmu, mu girmama junan mu, koda kuwa munfi ko an fimu shekaru.
Ta bangaren rayuwar mu da amawa kuwa, musan da wadanda zamuyi mu'amala, ina shan mamaki idan naga ko naji labarin sister mai kula samarin amawa, ko Mai soyayya da ba'ame, amtsayinki na yar sister da brother, takamar goyon hijabi,  har ki zauna kina bata lokacin ki da tara samari barkatai! Yanzu auri ka gyara ma ya kau, don sayyid (h) ma cewa yayi yanzu auri ka gyarama ya zama auri ka bata!. To bare kuma ke sister, ki auri ba'ame kice kinyi me? Ina tabbatar maki wallahi, tallahi, baillahillazi laaa'Ila ha'illahuwa wata rana sai kun wayi gari gwagwarmayar ma ya hanaki, kuma dole ki hanu ba yadda Kika iya!. Babu wata riba ga auren ama, don haka in abin in bamu shawara ne sai nace don Allah sisters mu tsaya kan yan uwanmu brothers don sune suka San ciwonmu, su zasu darajtamu, zasu bamu cikakkiyar kulawa, Wanda ama bazasu bamu ba.
Kodayake matsalar tana ga iyaye! (Kuyi min afuwa ba nufi na Baku laifi bane) ba yadda za'ai uba na gari ya dau auren yarsa ya bama na'ame, hakan ba wayewa bace, abinda nake so a fahimta anan.shine kuskure ka dauki yarka ka bama na'ame.

           Matsayin kwalliya ga sister

Wasu daga cikin sisters dinmu basu San menene kwalliya ba bare Susan yadda ake yinta. E kwarai kwalliya bamu ne mai kyau domin tsabta tana daga cikin imani, amma kisan a Ina ya kamata kiyi kwalliya kuma wa zakiyima. Abin takaici da ban haushi sai kaga sister taci ado duk ta bata fuskarta da powder, Jan baki, eye shadow, eye Lerner, kai abin dai ba kyan gani,  don Allah sister idan kinyi kwalliya kin fita wa zaki burge? Tarbiyar ki fa ta ban-banta da ta sauran yanmatan amawa, idan kinyi Ado kin fita ba abinda zakijama kanki sai tarin zunubai (wa'iyazubillah) domin wani idan ya ganki zaki burgeshi, wani zaiyi aha'awarki, kin ga ajinki ya zube, idan Kika ta shi fita kisan a yadda Saki fita wani ma duk iskancinsa sai yaji tsoron yi maki magana don zaki masa kwarjini ne.
Daga karshe don Allah sisters mu zama masu mahimmanta all'amuran harka islamiyya. Duk wasu lokutanmu ya zamana nayima harka islamiyya hidima ne, duk wani tunanin mu ya zama na cigaban harka islamiyya ne, sister ki tuna duk inda Kika shiga bakya boyuwa ga al'umma domin alaminki na hijabi, duk abinda kika aikata bazai boyu ga al'umma ba kuma kai tsaye zai koma ga sayyid ne, don haka kisan me zakiyi.

Ma'a sum ah Nigeria News Update 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post