Gwagwarmaya a tafarkin Allah:/ kashi na uku {3}

Ma'asumah Nigeria News Update
👉by sharhabil Usman pandoss

Akwai wani jawabi da su Jagora (H) suka yi wajen rufe mu'utamar a Maiduguri, a cikin jawabin sunyi bayanin menene gwagwarmaya da yadda ma'abota gwagwarmaya suke kasancewa. Shi ma'abocin gwagwarmaya yana da kyau ya san asasin manufarsa da abinda yake hankoro, wanda kuma wajen tabbatarda wannan hankoron nasa komi zai iya rasawa ya yadda kuma da hakan.

Duk mabiyinda ya amsa kiran Jagoransa ya aminta cewa wannan Jagoran nasa shine Jagoransa, shine wanda ya yadda ya mika ma hannun bai'arsa, to ya shirya ma Jarabawa na nan tafe, komi zai iya faruwa. Tafiyarsu Jagoranmu gaskiyar magana sai mun sallama jin dadin wannan duniya sannan ne za ta yi dai dai da ita, ta yadda idan jarabawa tazo da man mun san da zuwanta.

Yanzu haka maganar nan da muke yi akwai yan'uwa maza da mata da suka tare a Abuja ba dan komi ba, sai domin yan'cinsu Jagoranmu (H), ba kuma wai dan ba su da abinyi bane, da yawansu 'yan makaranta ne, wasu kuma suna harkokin kasuwancinsu a garuruwansu, amma suka yadda suka bari suka tattaro dan abinda suke da shi suka dawo zama a Abuja, suka yadda da rashi da tsanani da takurawa da tsangwama daga wajen makiya na ciki da na waje, su dai fatansu Jagora ya samu 'yan'cinsa.

Wane dan gwagwarmaya ne na gaskiya zaiji cewa wadannan bayin Allah al'amarinsu bai shafe shi ba? Sannan kuma zai kalle su a matsayin wasu mutane daban da shi, duk halinda suke ciki ba ruwansa har ya dinga masu kallon 'yan ta da zaune tsaye, ya gaza bayarda gudumuwarsa da karfafawarsa da iya karfinsa na abinda Allah ya hore masa na dukiya da lafiya da basira da iliminsa, 'a lokaci guda kuma yana kallon kansa a matsayin dan gwagwarmaya, anya wanda zaiji wannan ya ma fahimci abinda su Jagora (H) suke ma Jagoranci kuwa? Muna fatan 'yan'uwa hankalinmu ya dawo jikinmu, mu fuskanci gaskiya da ma'abotanta, mu yi fatan kuma samun sabati da taimakon Allah (T) har nasara ta zo mana.

— 23/01/2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post