@Ma'sumah Nigerian News Update@
-Duba da lalace war Jami'a da yadda muke tafiyar da rayuwa ba tsari yakama ta musan fa! addini ne ya kawo mu wannan duniyar, an halicce mu ne domin mu bautawa Allah (T) .
-Mai zai hana mu dabbaka hakkaan a dukkan muhallin da muka tsinci kanmu ciki, domin sauke nauyin wannan addini da samun tsira gobe kiyama. Yana da kyau Musani a dukkan waruren da muke rayuwa akwai masu farautar imani wadanda su ba hadafin su addini bane.
-Hasali ma ba'a dora su kan wannan turbar ba, Shikenen don kuma bama tare da iyayenmu a kusa musamman masu zaman Campus sai ya Zamana munyi watsi da tarbiyar da aka gina mu akai tun tasowarmu?.
-Matuqar mukai hakan munci amanar iyayenmu da kuma Allah, kuma lallai, iyayenmu zasu Kalubalance mu gaba ga Allah kan sun tarbiyyan tar damu amma karshe mun lalata wannan tarbiyya din, mun zabi rudun duniya da kauce wa hanya madaidaiciya.
-A karshe ina kara kira da babbar murya cewa, yan uwa na maza da mata mu dawo hayyacinmu mu damfaru fa addini a zukatanmu da ayyyukanmu domin samun tsira ranar lahira hakan shine kadai mafitarmu.
-Tammat bi hamdillah, Allah ya kara karemu daga fadawa aiyukan halaka, ya tsare mu ya tsare imaninmu, ya kara mana soyayya ga iyalan gidan Manzon Allah (S).
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈