
Ko akan wani dalili aka daure har mutane 7 ?.
Daga Wakilin Mu --Idishia Jos.
Babbar kotun Jihar Kwara wacce ke zama a Ilorin, a ranar Laraban nan ta daure wasu mutane Bakwai a bisa samun su da laifin yin safarar sassan Jikin mutane, gami da mugunyar sana’ar siye da sayar da sassan jikin na dan adam ga masu bukatar yin tsaface-tsaface domin neman kudi.
Mutanan da aka dauren sun hada da wani mai siyar da maganin gargajiya, Bokan da ke aikin hada masu tsafin, wani dalibin makaranta da kuma wasu mutane hudu. Sun kuma aikata laifin ne tun a shekarar 2017 a Ilorin.
Sunayen mutanan da aka dauren sun hada da, Azeez Yakubu, Aishat Yinusa, Lukman Saka, AbdulGaniyu Bamidele, Ahmed Yahaya, Saliu Ayinde da Abdulrasak Babamale.
Wanda ake tuhumar na farko mai suna Azeez Yakubu, an daure shi ne tsawon shekaru 15, sa’ilin kuma da aka daure sauran mutanan shekaru goma-goma kowannen su. Laifin da suka aikata ya shafi hada baki, safara da mallakan kokon kawunan mutane har guda 11, kasusuwan kasan bakin mutum guda 11, tulun gashi na maza da na mata, kasusuwan mutane wadanda aka hako daga makabartu daban-daban a Ilorin. Kafin a yanke hukuncin, shaida na farko mai suna, Mohammed Kamaldeen, wanda sajen din ëyan sanda ne, ya bayar da shaidar cewa a ranar 5 ga watan Oktoba, 2018, an kawo ma su karar hadin baki da kuma siyar da sassan jikin dan adam, a ofishin su na ëyan sanda da ke Adewole.
Ya kara da cewa, wanda ake tuhuman na farko mai suna Yakubu, an kama shi ne da kokon kawunan mutane guda Bakwai, kasusuwa da tarin gashin mutane. A cewar mai gabatar da karan, an aike da dukkanin kayayyakin da aka kama su da su zuwa Asbitin koyarwa na Jami’ar Ilorin domin a tabbatar da cewa lallai na dan adam ne, a bayan kuma binciken an tabbatar da cewa duk an tsinko su ne daga sassan jikin ëyan adam. Wani kuma mai bayar da shaidar mai suna, Matthew Omotosho, ya shaida wa kotun cewa yana daga cikin tawagar jami’an tsaron da suka je suka kamo wadanda aka dauren.
Alkalin kotun ya kwatanta mugun aikin masu laifin da cewa ya munana, kuma abin kunya ne, daganan sai ya daure wanda ake tuhuman na farko Azeez Yakubu, shekaru 15 tare da tarar Naira 100,000 kowannensu.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.