@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ZAMA A RAKA'AR FARKO KAFIN MIQEWA TA BIYU SUNNAH CE BISA RIWAYAR BUKHARI .
Nayi nufin wannan rubutu ne kawai don na nunawa wasu mutane abinda iliminsu bai kai gare shi ba, kuma suke qoqarin sukar masu aikata wannan sunnah bisa rashin sani.
Bisa ittifaqi ma malamai shine, duk wani abinda Annabi (S.A.W.W )yayi ko yayi umarni da yinsa ko kuma yaga an aikata a gabansa bai hana ba, to, wannan abu ya zama sunnah, sai dai wanda yaga dama ya aikata , wanda kuma,yaga dama ya kangarewa mata.
Masu irin wannan tunani sune masu ganin Annabi (S.A.W.W )na iya aikata wani abu cikin fitar hayyacinsa, kamar dai yadda suka fada a kansa yayim da yayi umarni a kawo masa abin rubutu ya rubuta wasiyyarsa .
GA DAI RIWAYOYIN KAMAR HAKA
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(i )- Bukhari ya riwaito cewa, Musa Bn Isma'il ya bamu labari, Wuhaib ya bamu labari yace, Ayuba ya bamu labari daga baban Qilabata yace, Malik Bn Huwairith ya zo mana cikin wannan masallaci, sai yace;
‘’ NI ZAN YI MUKU SALLAH, BA WAI SALLAR NAKE NUFI BA SAI DAI ZAN YI SALLAH YADDA NAGA ANNABI (S.A.W.W )YAKE YIN SALLAH.‘’
Sai muka cewa baban Qilabata , to, yaya yake yin sallar? Sai yace;
‘’ MISALIN WANNAN MALAMIN NAMU !‘’ Yace,
‘’ MALAMIN YA KASANCE YANA ZAMA YAYIN DA YA 'DAGO KANSA DAGA SUJADAH KAFIN YA MIQE DAGA RAKA'AR FARKO .‘’
Manuni
(KITABIL AAZAN , BABI NA 45, WANDA KE MAGANA KAN ‘’ WANDA YA YIWA MUTANE SALLAJ DON YA KOYAR DA SU SALLAR ANNABI (S.A.W.W )DA KUMA SUNNARSA. HADISI NA 677).
(ii )- A wata riwayar kuma yace ;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ IDAN YA 'DAGO KANSA DAGA SUJADAH TA BIYU YAKAN ZAUNA YA DAIDAITA AKAN QASA, SANNAN YA MIQE.‘’
(Bukhari , hadisi me lamba 824).
IDAN BA IRINTA KAKE YI BA, TO, BA DA ANNABI (S.A.W.W )KAKE YIN,KOYI BA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~26th January , 2020.
Tags:
Taskar ilimi