Shahadar Qaseem Suleiman:/ Sabbin bayanai gameda shahadar su,:


Ma'asumah Nigerian news updates
👉by sharhabil Usman pandoss

ALLAH YA KADDARA ABUN YA FARU SAI YA FARUN.
.
Jagoran bangaren kula da sararin samaniya, na rundunar kare juyin Musulunci a Iran, Haji Ali Zadah ya baiyana a jiya Laraba cewa, Amurka ta yi amfani da dabaru da dama wajen aiwatar da kisan sa ta yiwa su janar Sulaimaniy, kuma dakarunsa sun kasance suna dako tare da bibiyar duk wani motsi na Amurkan a cikin Iraqin, sai dai a wannan lokacin, basu san takamaimen abinda Amurkan ke nufin aiwatarwa ba kenan.
.
Game da kashe Sulaimaniy, Zadah ya ce Amurkawan sun yi amfani da kayan aiki iri daban-daban, dan ganin su kai ga kashe Sulaimaniy, saboda basu da masaniya, game da sauye-sauyen da aka aiwatar, da ya shafi adadin motocin da suka zo tarbarsa a filin jirgin saman.
.
Kanfanin dillancin labaran Iran, FARS, ya riwaito Haji Zadah yana cewa babu shakka al'amarin ya bada mamaki kwarai, saboda mun kasance muna biye da duk wani motsin Amurkawan, ta yadda mun san da tashin wani adadi mai yawa na jiragen yakinsu, dauke da guzurin makamai masu nauyi, muna kuma biye da su, sai dai bamu san takamaime me suke nufin yi ba. Mun ga bayan jiragen sun tashi, ana ta kara tura masu makamashi, mun kuma ga wani adadi mai yawa na jirage marasa matuki samfurin MQ9, wadanda mafi yawa sun taso ne daga sansanin sojan Salim, da ke kasar Kuwaiti.

Zadah ya kara da cewa wani adadi na jiragen Helkwafta suma sun taso daga wasu sansanonin sojan Amurka da ke cikin Iraqi, kamar sansanin al-Tajiy, da na Ain al-Asad, adunkule muna iya cewa sansanonin soja 4-5 ne, suka yi taraiya wajen aikata wannan ta'addancin, kuma dukkansu muna biye da su ta hanyar na'ura, sai dai bamu da masaniya game da takamaimen abinda suke son aiwatarwa.
Zadah ya ce a dai-dai wani lokaci, jiragen yakin Amurka, samfurin F15, suna kai komo a tazarar kilomita 40-50 tsakaninsu da Bagdad, sun kasance suna tafiyar kimanin kilomita 1100 a awa daya, bayan sun matso kusa da Bagdad, sai kuma su sake komawa, sai muka lura akwai abinda suke jira.
.
Ya ce cikin aikin bin diddigin da muke, muka gano wani jirgi maras matuki samfurin MQ9, da aka baiwa wani aiki, amma jirgin ya rika samun matsalar amfani da makaman da yake dauke da su. Jirgin ya rika tattaunawa da wadanda ke sarrafa shi daga nesa, sai dai duk bamu kai ga gano cewa manufarsu, ita ce kai wa janar Sulaimaniy hari ba, sai dai bayan mun harhada wadannan bayanan wuri guda, mun gano sansanoni 4 ne ke da hannu wajen aikata wannan ta'addanci.
.
KO WANNAN YANA NUFIN KENAN WADANNAN SANSANONI YA KAMATA SU BIYA FARASHIN AIKIN DA SUKA AIWARA? KAWANAKI MASU ZUWA NE ZASU AMSA WANNAN TAMBAYAR.
_13/01 /2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post