majalisar wakilai ta bukaci shugabannin tsaro da su yi murabus


A cewarsa, kasar za ta kasance cikin hatsari idan aka bar wadannan mutane suna cigaba da maimaita abu guda tare da sa ran samun banbancin sakamako wajen yaki da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.
Da yake jagorantar zaman, kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila ya karanto ayar tambayar da Fulata ya dasa ga yan majalisa kan ko shugabannin tsaron su yi murabus daga kujerunsu.
da dai an samu rabuwar kai a tsakanin yan Majalisar wajen bayar da amsoshinsu, mafi rinjaye na yan majalisar sun amince da hakan sannan aka aiwatar da hukuncin
A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa Wasu sanatoci sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami shugabannin tsaro na kasar.
Sun kuma yi kira ga murabus din sufeto janar na yansanda, Mohammed Adamu.
Yan majalisar sun gabatar da bukatar ne a gudunmawarsu kan tattaunawa da aka yi game da lamarin tsaro a kasar a lokacin zaman majalisa a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu.
Wadanda suka yi wannan kira sun hada da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, sanata Musa Sani, Betty Apiafi da Solomon Adeola.
Yayinda sanata Sani ya yi kira ga murabus din Shugaban yan sanda, Apiafi da Adeola sun bukaci shugaban kasar da ya tsige dukkanin shugabannin tsaro.
A cewar yan majalisar, ya kamata a sauya shugabannin tsaron tunda basuda sabbin dubaro na yaqi da yan ta'adda.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post