Wanda Ya rasa Uwa yayi Babbar Hasara !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

ITA TA FI SANIN SHIRUN 'YA'YATENTA

Uwa da Uba sune babban gata ga duk wani abin haihuwa ko da kuwa a cikin dabbobi nene. Wanda ya rasa daya daga cikin su ya yi babbar  hasara wacce babu abinda zai samu wanda zai maye  gurbin su.

Duk kyautatawar miji ko mata ga abokin zama ba zai taba kasancewa a matsayin dayan  mahaifa ba, domin kuwa ana iya canza su.

Cikin  iyaye kuma babu kamar uwa wajen qauna, tausayi  da kuma kyautatawa 'ya'yayensu. Uwa ita ce wacce za ta sadaukar da komai nata don ganin ta farantawa 'ya'yayenta ba tare da ta damu  ba.

 Ita ce wacce ba ta qyashin dukkan abinda  'ya'yanta za su samu.

Ita ce  wacce ke sauraren dukkan koke n 'ya'yayenta  da kuma sanin damuwarsu .

Ita ce wacce ke iya fahintar shirun 'ya'yayenta ba tare da sun bayyana  mata abinda ke damunsu ba.

Ita ce wacce ke tarbiyyantar da 'ya'yayenta kan kyawawan  dabi'u.

WANDA YA RASA UWA YA YI BABBAR HASARA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah  Guda  .

       08126385470

~17th December , 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post