TSAKA MAI WUYA:- Sakin Sayyid Zakzaky ko Cigaba da Tsare Shi ??




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS  UPDATED @Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

SAKIN SAYYID ZAKZAKY (H )KO CIGABA DA TSARE SHI

Hausawa suka ce, " BA KA JIN ZAFIN CIWO IN BA A JIKIN KA YAKE BA ". Tabbas wannan magana haka take ga wadanda ba muminai ba, amma ciwon  mumini na mumini ne ko da kuwa a wanne guri yake .

Idan muka yi amfani da wannan karin magana na hausawa sai muce eh lalle kuwa talakawa  da qananan almajirai masu bin wasu maluma a matsayin jagororin su ba su san zafin ciwon da ke jikin gwamnati , sarakuna da kuma malamansu  masu adawa da da'awar Sayyid Zazkzaky (H )ba .

Su wadannan jinsin mutane, gwamnati da sarakuna da kuma maluma suna cikin tsaka mai wuya game da al'amarin sakin Sayyid Zakzaky  (H )ko kuma cigaba da tsare shi.

Sun aikata babban kuskure a gurare biyu wanda yanzu ya zame musu  tashin hankali da rashin nutsuwa tare da su , sai dai wadanda ke ganin ayyukan wadannan gungun mutane a matsayin daidai ba su san haka ba.

Kuskuren su na farko shine , dirar da suka yiwa Sayyid  (H )da nufin kashe shi , sai Allah ya nuna musu cewa rai a hannunsa  (T )yake ba hannunsu ba , kuma  sun kasa yin abinda suka yi nufin yi a kansa (kisa ).

Kuskurensu na biyu kuma shine , yayin da kotun dake qarqashinsu ta yanke hukuncin cewa su saki  Sayyid (H )tare da biyan diyya gare shi a matsayin keta alfarma da take masa haqqinsa na dan Adam kuma dan qasa mai ikon yin addininsa gwargwadon yadda ya fahinta .

Wannan abubuwa biyu sun janyo musu jin  kunya a idon duniya da kuma cikin wannan qasa tamu Nigeria .

Yanzu sun rasa yadda za suyi da shi ta yadda za su sami mutunci a idon duniya da kuma idon wadanda suke ganin qimar su .

Akwai  jin kunya cikin cigaba da tsare shi don ba su da hujja ko dalili , sannan kuma akwai qasqanci cikin sakinsa , domin babu abinda za su dogara da shi a matsayin dalili . Wannan abu ya jefa su cikin tsaka mai wuya ta rashin sanin makama , shi yasa kuke ganin suna yin abinda suke yi.

Su kuma wawaye suna ganin aikin nasu  a matsayin aikin jaruntaka ko kuma masu yin abinda ya fi dacewa ga jagoran muslimci  Sayyid Zakzaky  (H ).

MU DAI MUN CIGABA DA ADDU'AH, DA MUZAHARORI , ALLAH KUMANA YIN ABINDA YA FI DACEWA .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

          08126385470

~ 16th December , 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post