Tunkarar zalunci shi ne babban abin da zamu koya daga Sayyida Zahra


- Cewar Malama Zinatuddeen Ibraheem.

Daga Ammar Muhammad Rajab.
“Babban abin da Sayyida Zahra ta koya mana
shi ne; mu tsaya mu kori zalunci. Mu cema
azzalumi azzalumi ne. Tunkarar zalunci shi ne
Babban abin da zamu koya daga Sayyida
Zahra.”
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Malama
Zeenatudeen Ibrahim a lokacin da take
gabatar da jawabi ga cincirindon dubun-
dubatar al’ummar Musulmin da suka taru a
filin polo daura da Husainiyyah Bakiyyatullah,
Zariya jim kadan da kammala muzaharar
maulidin Sayyida Fatimatuz Zahra (sa) da ya
gudana a jiya Juma’a.
Tun farkon jawabinta, Malamar ta fara ne da
taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar
wannan rana ta haihuwar Sayyidatin Nisa’il
Alamin, Fatimatuz Zahra (sa). Sannan ta
tunatar da al’umma manufar hallittarsu zuwa
doron kasa. Sannan ta yi nuni da yadda tun
kafin a aiko mu wannan duniya domin mu
bautawa Allah ta’ala, Allah ya yi ma
halittunsa tayi, kowa ya ce a yi masa uzuri,
amma dan Adam ya ce zai iya. Sai ta ce;
Allah ta’ala ya yi hakan nan ne domin ya
sakantama Muminai maza da mata da
azabtar da munafukai maza da mata.
Sai ta yi nuni da yadda mutum ya siffantu da
matsaloli biyu. Matsalar farko ita ce; ya zo da
abokin gaba wato shaidan, ga kuma matsalar
kanka (son rai). Ta ce; wannan ne yasa ake
aiko Annabawa domin tunatar da wannan
amana din da dan Adama ya daukowa kasan.
Har ila yau a wani bangare na jawabinta, ta
ce; kowane Annabi idan zai tafi sai ya bar
wasiyyinsa.
Da ta juyo dangane da wannan Annabin kuwa,
ta yi nuni da yadda Manzon Allah (saww)
cikin shekaru 23 ya canza al’umma masu
busassun zukata. Sai ta ce; wannan canjin na
Manzon Allah, mu’ujiza ce. Sannan ta yi nuni
da yadda Manzon Allah ya bar wasiyyansa 12
a bayansa. Daya bayan daya. Ta ce; kamar
sauran Annabawa,a duk lokacin da suka bar
wasiyyi, sai a samu ‘yan tawaye, haka suma
wannan al’umma suka bijirewa wasiyyin
Manzon Allah.
Da ta juyo dangane da kafircin duniya kuwa,

cewa ta yi; idan muka yi la’akari, yanzu
kafircin duniya sun haukace, sun haddasa
fitina a kasashen Musulmi da dama. Ta ce;
wannan haukacewar ya nuna cewa; suna
ganin karshen su ya zo. Sannan sai ta
jaddada cewa; wannan lokacin da yanzu
zalunci ya tunkaromu, kuma ya mamaye
ko’ina, yanzu ne lokacin tsayawa akan
wannan darasi na Sayyida Zahra. Na tsayawa
a gaban azzalumi ka ce masa azzalumi ne.
Sannan ta ci gaba da cewa; iya abin da
azzalumai zasu iya yi shi ne kisa.
Sannan ta yi bayanin yadda azzalumai a kulli
yaumin suke ta yunkurin ganin sun kashe
Malam (H). Sannan sai ta shawarce ‘yan uwa
tare da kiransu da cewa; dole ne ya zama
wannan darasin da Sayyida Fatimatuz Zahra
ta bari, wanda ‘ya’yanta suka dauka, idan da
gaske muke, har kuma muna so Sayyida Zahra
ta yarda damu, ta yi mana juwari a gaban
Manzon Allah, to dole ne mu raya tsayawar da
ta yi ta kuma tunkari zalunci.
Daga karshe ta shawarci ‘yan uwa mata da su
rika farin ciki da abin da ya dace da shari’a. a
gu ji sabama Allah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post