Tsintuwa Guda Biyu Gidan Ali da Fatima (as) Cikin AlQur'ani da Hadisan A'imma



lokacin da Fatima ta yi rashin lafiya mai tsanan ta zauna tsawon kwanaki arba'ain cikin rashin lafiya, yayin da ta debe tsammani daga rayuwa.......
_____________________________

Hakkinne akanka idan kakaranta kayi shere domin Mafanar wasu.

    ~Daga Ishaq Mohd Kibiya

   _Bisimillahir Rahamanir Rahem_

mafi darajar tarihin tarbiyyar iyali shi ne tarihin rayuwar ali (as) da matarsa Fatima (as) haqiqa tarihin rayuwarsu tarihin rayuwa ne na ma'asumai biyu wadanda zancensu da ayyukansu da abubuwan da suka zartar dukkaninsu na daga cikin sunna mai daraja, ba zaka taba samun iyali da suke dauke da ismar zati da dukkanin sasanninta da bangarorinta sai gidan ali da fatima (as) rayuwarsu ta aure ita ce mafi alherin misali da kasantuwa abar kwaikawayo, cikin rayuwarsu akwai wani abin tsintuwa da ke yada haske da kyawu da rayuwa da nishadi, za mu koyi yanda ya kamata mu rayu qaqa zamu dinga tunani a matsayinmu na ma'aurata da sukayi sa'a cikin rayuwar aure da duniyar iyali da tarbiyya da koyarwa.

daga cikin ababen tsinta:
yayin da abubakar da umar suka yi niyyar ziyartar fatima (as) lokacin rashin lafiyarta sun nemi izinin ali (as) sai ya shiga wajenta ya ce mata: ya ke `yantacciya haqiqa wane da wane suna qofar gida suna jira suna son gaishe ki amma me kika gani ? sai tace gida gidanka ne sannan `yantacciya taka ce matarka ce, kana iya yin yadda ka so.
wannan tsintuwa na da matuqar qayatarwa cikin rayuwar aure, lalle wannan tsintuwa na ishara ga ma'aurata ta yaya fuskantar juna zai kasance tsakaninsu da kuma yanda za su yi mu'amala da juna, ga wanda ya nufi shigar da baqo cikin gida kan wani batu na siyasa ya kamata ya nemi izinin matarsa ya bata labari ya ji ra'ayinta kan batun saboda ta na da haqqi kan gida da abin da ke gudana cikinsa, sannan ita kuma ya kamata ta girmama matakin da zai dauka ka da ta kalli kanta bakin komai gaban mijinta, ta ce masa gidanka ne ni kuma mallakarka ce ka aikata dukkanin abin da ka ga ya dace,

daga cikin kyawawan tsintuwa daga gidan ali da Fatima {as} shi ne abin da ya zo cikin wasiyyar zahara (as) lalle ita ta bayyana rukunan asasi cikin rayuwar aure ta koyar da dukkanin mutane da matan duniya yaya mace za ta kasance cikin gidan mijinta da menene aikinta a addinnance da mutunce, lalle da mace za ta yi ado da wadanan siffofi da ta rayu cikin arziqi ta mutu cikinsa da soyayya qauna da tausasawa sun zama jagaba cikin rayuwarta, rabuwa da ita ya girmama wajen mijinta.

 lokacin da Fatima ta yi rashin lafiya mai tsanan ta zauna tsawon kwanaki arba'ain cikin rashin lafiya, yayin da ta debe tsammani daga rayuwa, sai ta cewa da ali (as) ya dan baffana lalle raina ya sanar da ni mutuwa ta, lalle ni ina ganin babu abin da ya rage gareni face riskar babana cikin kowanne lokaci, ina maka wasiyya da wasu abubuwa da ke cikin zuciyata, sai ali (as) ya ce mata: kiyi wasiyya da dukkanin abin da ki ke so ya `yar manzon Allah (saw) sai ya zauna kusada kanta ya fitar da mutanen da suke cikin gidan, sannan ta ce: ya dan baffana ba ka sameni maqaryaciya ko maha'inciya tun lokacin da ka aureni, sai ali (as) ya ce muna neman tsarin ubangiji daga haka lalle ke kimfi kowa sanin daga Allah da biyayya da karamci da tsananin tsoron Allah daga kasantuwar ace na zargeki da saba mini, lalle rabuwa da rashinki na da tsanani gareni sai dai cewa al'amari ne da babu makawa daga gareshi, wallahi musibar zafin rabuwa da manzon Allah (saw) ta qara sabunta gareni haqiqa rashinki da rabuwa da ke ya girmaa gareni, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un daga musiba me ya fita girma da radadi da zartuwa da baqin ciki, wannan wallahi wata musiba ce da ba ta ta'aziyyarta, sai suka fashe da kuka zuwa dani wani lokaci.
haqiqa Fatima (as) ta tattare rayuwar aure cikin wannan tattaunawa ta malakutiyya zuwa rukunai uku:
1 – rashin qarya 2 – rashin ha'inci 2 – rashin sabawa miji.

sai ta tunatar da sarkin muminai ali (as) da'arta da tsarkakarta da sallamawarta ga mijinta, shi kuma imam (as) ya yi godiya ga kiyaye alqawarinta ya kuma yi yabo kan tsarkakarta da juriyarta da taqawarta, ya bayyana mata soyayyarsa da qaunarsa da ratayarsa gareta, haqaia kalmominsa gareta kalmomine da suke motsa soyayya da girmama ga matarsa wacce babu wata mace kamar ta dukkanin fadin duniya.
bayan sun gama kuka sai ali (as) ya kama kanta ya sanya shi kan qirjinsa ya rungume sannan ya ce: kiyi mini wasiyya da dukkanin abin da ki ke so, tabbas za ki sameni mai zartar da wasiyyarki kamar yanda ki ka umarce ni, ki zabi al'amarinki kan al'amarina.

na'am haka rayuwar aure azurtacce ta ke ka ga miji ya zabi fifita abin da matarsa ke so kan abin da zuciyarsa ke so matuqar matarsa na tsoran Allah, kamar yadda zaka samu mace ta na fifita abin da mijinta ke so kan abin da ta ke so matuqar mijin na ta mai da'a ne ga Allah mai tsarkake niyya, zuwa misalin wannan rayuwar ma'aurata muke kiran baki dayan mutane tabbas za su samu arziqin gida biyu duniya da lahira


~Free Syed Zakzaky dolee

~Daga Ishaq Mohd kibiya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post