Mine Ma'anar Sunnah ???


Shaikh Ibraheem Zakzaky yace:
“Sunnah din nan tana da ma’anoni daban-daban; Akwai Sunnah na cewa; wani abin da ba farilla ba, akwai Sunnah na ma’anar cewa; abin da Manzan Allah (S) ya koyar ta hanyar zantukansa da ayyukansa da tabbatarwarsa, akwai sunnah na ma’anar jama’a, wanda yake nufin mutanen da suka dauka Annabi (S) bai yi wasiyya ba da zai rasu ya rasu ne kawai al’umma suka zabi jagora. To, in da bambanci, nan ne aka bambanta da Shi’a.

“Su kuma Shi’a suna ganin, a’a, Annabi ya yi wasiyya, ya ce; bayan sa ga wanda za a bi, ba ma guda daya, har zuwa ranar Al-kiyama, da umarni daga wajen Allah (SWT).
“Wa’nnan makarantu guda biyu, in kai Musulmi ne wanda ka damu kasan addini, ya kamata ka je ga littattafan kowacce makaranta ka ji ra’ayinta, ka dauki na dauka ka yar da na yarwa. To, mu kuma abin da muke yi kenan, duk abin da aka gada na Musulunci, to, na gadanmu ne, zamu duba ne mu gani, wanne ne ya yi dai dai mu dauka, wanda bai yi dai dai ba, mu ajiye, ko a makarantan wane ne. In na Shi’a ne, muna dauka muna wurgarwa. Na Sunnah muna dauka muna wurgarwa. Wanda ya dace, wanda Annabi ya zo da shi, shi ne addini.”

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post