Sirrin Warakar dukkan cuta, daga bakin Imam Ali (As)



Bismillahir Rahmanir Rahim...

Cuta wata jarrabawa ce da Allah keyi wa bayinsa na gargaru domin gwada imaninsu, amma sau tari yanayi ke haifar mana da wasu mafi yawan cututtukan ko kuma rashin kiyaye wa daga garemu domin koda jarrabawa ce din yakan zam akwai sila.

Mun kawo muku wata tsaraba ce daga babban masanin nan Wasiyyin Annabin Tsira Imamu Aliyu (As) yayin da yake magana da dansa Imam Hasan Al-mujtaba (As).

Imam din yake cewa; "Ya Hasan bana sanar dakai wasu hanyoyi guda hudu ba da in ka kiyaye su, zai zama na baka da bukatar neman magani ga dukkan wata cuta ba?"

Sai Imam Hasan yace; "Eh" Imam Ali yaci gaba da cewa; "Abu na farko kada ka zauna don cin abinci har sai kana jin yunwa, na biyu kuma, kada kabar wajen cin abincin alhali baka koshi dashi ba. Sai abu na uku ka tattamna abincin sosai cikin bakinka kafin hadiye wa,  idan zaka kwanta barci kuma ka gabato da ruwa kusa dakai.

Idan ka kasance kana aikata haka zaka kasance baka da bukatar wani magani ko masanin ciwo ya duba ka."

Zama da lafiya shine abin fatanmu gareku ya yan uwa. Allah ya bawa mara sa lafiyan mu lafiya, ya kwato mana su Sayyid (H) a hannun azzalumai cikin lafiya da nisan kwana.

Su kuma azzalumai Allah ya kara kara kansu ya hana musu kwanciyar hankali duniya da lahira, Ya masanin komi kasan sun cutata mana kadau mana fansa ya Allah.

Daga wakilanmu na Saminaka. Tare da
Bin Haroun Sigau
08065008703.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post