Wasu na Shan Bakar Wahala wajen Neman Amincewar Yar dar Macce !!!


Matsayin ka Shi ne Qimar Ka a wajen ta
_________________________________
@ MA'ASUMAH  NIGERIAN NEWS  UPDATED
@ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
__________________________________

Duk abinda mutum ke so ya kanyi qoqarin don ganin samun wannan abu , sai dai hanyoyin da ake bi ne sun kasu gida biyu .

Wani lokaci wani kan bi mummuniyar hanya don ganin buqatarsa ta biya ko da kuwa ta hanyar sabawa nahaliccinsa ne, wani kuma kan bi kyakkyawuyar hanya ce don samun wannan abin .

A yanayin nema na aure bai kamata ace ka yiwa mace dole ba , matuqar ka nemi yardarta kuma ta qi , to, kayi haquri ba sai ka bi mummuniyar hanya don ganin ka sami matsuguni cikin birnin zuciyarta.

Matsayinka a wajenta shine gwargwadon qimarka cikin zuciyarta , idan ba kayi sa'ar shiga zuciyarta ba kuma ka nace kan a dole sai ka sami karbuwa wajenta , to , ko da ace akwai sauran mutuncinka a idonta zai kauce , kuma za ka cutar da ita .

Hakama ke mace, kada ki ce dole sai kin sami karbuwa cikin zuciyar wanda bai shirya karbar ki ba, idan kina da qima a wajensa shi zai yi qoqarin ganin ya samar miki wajen shaqatawa  cikin  lambun zuciyarsa , amma kuskure ne kice dole sai ya so ki .

SABODA HAKA BABU TILASCI A SOYAYYA.

Tare da Ado Isah Guda .

08126385470-08137925034

~16th  December , 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post