ALLAH YASA GWAMNATIN TARAYYA TASAWA GIDAN YARIN DAURA, SUNAN MARIGAYI YARIN DAURA NA FARKO MUSA(YARI MUSA). YARI MUSA CORRECTIONAL CENTER.
Rubutu na, na yau ba karatun raggo bane domin tarihin gidanmu ne zan bada don haka sai mutum ya shirya kafin ya iya karanta shi.
WANENE YARI MUSA?
Muhammadu(Wanda akewa lakabin Muhammadu Giwa) mutumin Rogogo chidari ne tanan kasar Daura, wadda yanzu take a karamar hukumar zangon Daura, shine mahaifin MUSA YARI.
An haifi Musa a cikin shekarun 1870s wato kimanin shekara Dari da hamsin da suka wuce a garin Rogogo chidari kamar yadda nayi bayani, amma a lokacin ana kufai, nan kudu maso yamma kadan da inda garin yake yanzu.(wato tsohon gari kafin su dawo kan tudu lokacin da ruwa yacisu)anan ya tashi ya girma har yayi aurensa na fari ya kuma haifi kakanmu Alhaji Abdullahi Wanda shi kuma ya haifi Babana/mahaifina IBRAHIM/NUHU, da sauransu.
Musa ya kasance manomi kuma dan kasuwa, domin a lokacin kaf kasar Daura babu masu harkar fata da kirgi tun kafin zuwan turawa har lokacin da suka bayyana, a lokacin suna wannan Sana'a ne shi da dan uwansa Alhaji Abubakar Wanda akewa lakabi da sunan Alhaji Rumbu(Runbun kudi na malam Darhu) yasamu wannan suna ne sakamakon arzikin da allah yayi masa a lokacin ana hasashen kaf kasar Daura ta gabas babu mai arzikin Alhaji Abubakar (Rumbu) Wanda sakamakon haka har sunan sa na yanka ya bace saidai ace ALHAJI RUMBU, wannan labarin bawai ba inke,duk Wanda ya rayuwa a wancan lokacin yasan haka, kakanninmu sun fadamana cewa Alhaji Rumbu har hawan dawaki yake shiryawa kamar hawan sallah, saboda kasaita ta arziki.
Musa shida dan uwansa sun kasance suna sayen fata a karkarar dake zagaye dasu idan sun tarata shi Musa a matsayinsa na karami yake daukarta yakai kano jalla babbar Hausa ya sayar ya dauro kudinsa ya dawo. Ana cikin wannan halin ne wata rana Rumbu yayi cinikin wata fata ba'a sallama masa ba, ya wuce, shi kuma Musa ya kawo kai ya saya akace haka dan uwanka ya saya ba'a sallama masa ba, don haka sai shi kuma yayi Kari aka saida masa, wannan ciniki baiwa Rumbu dadi ba, don haka ya hau Musa da fada, Wanda hakan yabatawa Musa rai dama gaya da zuciya sai ya watsa masa kayansa yace kaifa nakewa wahala kuma fatar nan da aka saya ba asara za'ayi ba don haka ga kayan ka nan, wannan shine karshen kasuwancin Musa da dan uwansa.
MUSA YABAR GIDA.
Sakamakon wannan takaddama tasa Musa barin gida ya shiga duniya domin Neman sa'a, daya tashi bai zame ko ina ba sai birnin kano, tunda dama yasaba zuwa, anan ya sauka wajan abokan mu'amullarsa, aka kumayi sa'a ana daukar sojoji masu zuwa yakin duniya na daya karkashin sojojin birtaniya. Don haka Musa baiyi wata-wata ba sai ya fada aikin soja inda suka runkuta bakin daga bayan samun horo na dan gajeren lokaci. Daga nan ya shiga fagen daga tun daga farko har karshen yaki inda aka gwabza yaki na kusan shekara uku da rabi daga 28-july-1914 zuwa 11-November-1918, Allah cikin ikonsa akayi yaki lafiya aka gama lafiya batare da samun wata lurara ba.
Bayan gama yaki suka dawo gida najeriya inda sukaci gaba da zama karkashin sojojin England(Burtaniya), yana a matsayin sergeant na soja, daga nan sai sunan sa ya sauya daga Musa zuwa sergeant Musa Daura(saja Musa Daura) yayi zama da shugabannin sojoji turawa na tsawon lokaci har zuwa farkon shekarun 1930, daga nan sai ya fara tunanin gida, saboda haka hankalinsa ya juyo zuwa ga iyalinsa. A lokacin ya nemi hukumar sojan burtaniya tasallameshi yanaso zai koma gida, sai sukace masa to a yanzu aikin da za'a baka idan ka koma gida yafi karfin garinku, don haka saidai ka zabi kano ko katsina ko Zaria akai ka can, sai yace ah! Ah! Bayason zama ko ina sai garinsu saboda kishin mahaifa, haka aka rubuto takarda aka bashi zuwa ga turawan mulkin mallaka na garin Daura. Anan aikin soja ya kare. Daya tashi dawowa gida ance yazo da abin duniya a lokacin babu mota sai jakuna,don haka saida yayo kayan jakuna goma sha biyu Niki Niki da kaya ya tunkaro garinsu Rogogo.
SAJA MUSA DAURA YAZAMA YARIN DAURA NA FARKO.
Murna babu kama hannun yaro wajan iyali, yan'uwa da sauran mutanen gari, domin tsawon lokaci babu Wanda yataba kojin labarin inda ya shiga bare wani yaje inda yake, bayan haka kuma baiyi dawowar yan yawon duniya na zamani ba aje a dawo kudin motama sai an aika maka kafin ka iso gida, shi da abin duniya yazo, kuma al'umma sun shaida haka domin ya rabarwa da yan'uwa aminai makwafta da kayayyakin dayazo dasu
Bayan Saja Musa ya huta hankali ya kwanta anyiwa juna barka da arziki, anyi labarai bayan rabuwa da jimamin abubuwan da suka faru, kwatsam! Sai ga marigayi sarkin Daura Abdurrahaman tare da baturen mulkin mallaka sunje Rogogo, saboda haka sai saja Musa yayi shiga ta kayan damara yaje wajan su tare dayin gaisuwa irin ta dakarun soja ya sarawa bature bayan amsar gaisuwa kuma ya mika masa takardar da aka bashi daga barikin sojan daya baro, bature ya daga takarda ya karanta sukayi murna shida sarki, daga nan aka nemi Saja Musa ya isa zuwa Daura.
A lokacin sai akayi sa'a dame yacire kan kaba an gama ginin gidan fursuna,(Gidan YARI ) na gabas da gari ba'a kai ga tarewa ba a shekarar 1934. Don haka saja Musa na zuwa Daura sai aka bashi mukamin YARI MUSA, inda yayi rantsuwar kama aiki batare da bata lokaci ba, daga nan sunan saja Musa yabata inda ya koma YARI MUSA DAURA.
YARI MUSA yakasance mutum ne jarumi Wanda baisan tsoro ba, kuma babu wasa a cikin aikin sa, baya kuma yarda aci amana bare a hada kai dashi a zalunci wani, bayan haka yana daidai da zamaninsa domin a lokacin mazaje sunayin suna ne ta hanyar tashi tsaye da asirai na kare kai da nuna Isa musamman a lokacin ilimin addini bai yawaita ba, kuma ko malaman zamanin basuyin hani da irin wannan tashi tsaye wajan Neman asiri da karon kai. Babana yataba bani labari shi kuma kakansa YARI MUSA yabashi labari cewa wata rana an taba bashi wani asiri lokacin yana Rogogo kafin ya tafi aikin soja, sai yaje gindin wata rijiya inda Fulani suke Jan ruwa domin ba shanu su, sun taru su da yawa kowa ya zura gugansa sunaja, sai YARI MUSA yaje ya kama gugunan dukansu yasa wuka ya yanke, duk suka fada rijiya, shi kuma yakoma gefe guda ya zauna, kasan bafulatani da bakar zuciya sai sukayo kansa da sanduna, nan take yadaka musu tsawa yace kai!!! Diyan Fulani kuyita dukan junanku kafin ayi haka duk sunyiwa juna rotse! Akayi sa'a can gefe akwai wani dattijon Bafulatani Wanda shima idonsa yake wanke, sai ya daka musu tsawa cewa kai! Sakarkaru magani ne yazo ya gwada akanku, daga nan sai hankalinsu ya dawo jikinsu, a lokacin shi YARI MUSA tuni yayi nisa. Haka suka tsaya suna kallonsa har ya bace.
Irin wannan tashi tsaye yana da yawa wajan YARI MUSA domin a lakocin yana gidan YARI babu wani mutum da za'a kawo ya gagara komai hatsabibancin mutum, komai tashi tsayen mutum idan yazo gaban YARI MUSA karyarsa ta kare, domin cewa yake a saki mutum a barshi a since idan ya isa ya gudu ga wajan nan, so da yawa barayi sun sha yunkurin gudu amma sai suzo soron gidansa su kwanta bayan sun baro cikin dakinsu, idan ya fito sallar asuba sai ya samesu nan kwance kofar gidansa dake nan gidan YARI. Wannan ya tunamin SARKIN MAKADAN SARKIN DAURA MARIKICINBAU, YAKANZO KOFAR GIDANMU YANA WA YARI MUSA WAKA BAYAN BAYADA RAI, CIKIN WAKAR AKWAI WANI BAITI DAYAKE DAUKAR HANKALINA,(inda yake cewa na Abu kura ba rago bace, wato hakan na nuna YARI MUSA ba abin wasa bane.)
Babu wani tawaye ko kangara da ta taba faruwa lokacin shugabancinsa domin ana tsananin tsoronsa, baya wasa da aikinsa kuma baya wasa da ma'aikaci akan aiki, amma kuma wannan bai hana shi kyautatawa daurarruba ta hanyar yimusu nasiha su zama mutanen kirki ta hanyar Jan hankalnsu su daina aikin barna, lokaci da dama iyaye na kawo kukansu wajansa idan an kawo diyansu yin sarka. Wannan tasa barayin ko sun bar gidan suke ganin girmansa, mahaifina yakan bani labari cewa DABO KWASARAWA Yakan biyo kofar gidanmu da yamma dagashi sai lagen gwado yazo ya gaida YARI MUSA lokacin yabar aiki,har ya kawo alkhairi yaba YARI, shi kuma yayimasa gargadin kada inji barna anan yace to Baba bazakaji Ba.
Abubuwa da dama sun afku na rikicin masu mulki a wancan zamani Wanda yajazawa wasu zuwa gidan YARI, saidai labarin bazai fadu a nan ba saboda wasu dalilai, amma tabbas YARI MUSA ya fuskanci kalubale a wannan lokaci saidai kasantuwar daga sama aka bashi aiki ba a kasar Daura ba, wannan tabashi damar tirjiya da bijerewa duk wani umarni da za'a bashi na ayi ba daidai ba koda kuwa daga bakin turawa ne bare kuma sarakuna. Wannan Gaskiya da rikon amana daya rike yakara masa girma da kwarjini a idon jama'a, SAIDAI ABIN TAKAICI GAYA TARIHI NA NEMAN MANCEWA DA IRINSU DOMIN BABU MAI TUNASU HASALIMA MUTANEN WANNAN ZAMANI BASU TABA SANIN ANIYI IRINSU BA.
YARI MUSA ya rike aiki da kyau yakuma kula da ma'aikatansa musamman ganin cewa ya haifi kusan dukkan abokan aikin sa, wannan tasa duk wata rigima idan ta faru a tsakanin ma'aikatansa da matansu, shike shara'a yaba mai gaskiya gaskiyar sa shiko marar gaskiya ya Dora fadin na tuba, a haka ya rike gidan YARI tsawon shekaru suna zaune shi da ma'aikatansa, gidansa yana daga gaba na sauran ma'aikata na bayansa.
Kuma wani abin burgewa dukkan diyan ma'aikatan gidan, YARI MUSA ya maidasu kamar jikokinsa shikesawa ayi musu Shayi,(kaciya kuma a gidansa ake jiyyarsu har SU warke) ALLAH YA SAKAMASU DA ALKHAIRIN SA. A farkon aikin ance ma'aikata goma sha dayane har shi YARI shiyasa Wanda yasan gidan YARI na Daura zaiga gida goma biyar daga Dama biyar daga Hagu sai kuma shi gidansa daga gaba yana kallon arewa.
GA WASU DAGA CIKIN SUNAYEN MA'AIKATAN NA FARKO, MAZA DA MATA.
1. Dan kaura
2.Aciye mamman
3. Kola sandamu
4. Sha'aibu Na Dari
5. Sule mato( chief sule)
6.Isa Yusuf(chief Isa)
7.Dan kallamu
8.Sale Usman (chief sale)
9.Nalema Yusuf
10.Ta sallah Doko
Wadannan wasu kenan daga mutanen da sukayi aiki da YARI MUSA, a lokacin dukkansu gajeren wando sukesawa a matsayin kaki (uniform) in banda YARI MUSA Wanda shi kadai kesa dogon wando, abin birgewa idan akace bature zaizo zagaye,(supervision)za'ayi ta wanki da guga goge takalmi da belt, ayi sitati da zargina yadda za'aga kyawon kowa a lokacin ana aiki bisa doka da tsari, Allah mai iko a yanzu dukkansu sun rigamu gidan gaskiya saidai fatan Allah yamusu gafara.
GA KUMA WASU DAGA CIKIN MASU LAIFIN DA AKA DAURE A LOKACIN MUSAMMAN MANYAN BARAYI.
1.Idi saida Gyada
2.Guyu Mamman.
3.Dabo kwasarawa
4.Dire Dan sale
5.Gamji
6.Balage zango
7.Ilu Dan Fulani
8.Na badake
9.Mamman kwanto
10.Isah Rufau.
Wadannan nadaga cikin manyan barayin wancan zamanin da YARI MUSA ya zauna dasu, kuma abin sha'awa ko wannesu akwai abin daya kware wajan sata, kamar SAIDA GYADA SATAR DOKI KAWAI YA KWARE DOMIN DA LIZZAMI YAKE YAWO, AKWAI WANDA YA KWARE WAJAN SATAR AWAKI, WANI SATAR GYADA, kai gasu nan dai haka, kuma suma shiryayyune da tsatsuba wani ya bace, wani ya shafa bango ya tsage, wani kuma idan yayo satar jajayen awaki sai su koma bakake, wani yakoma kyanwa, wani bera, Haka akayi ta fama dasu tsawon lokaci.
YARI MUSA shi ya assasa yin sallah akofar gidan YARI, lokacin malaminsa mai koya masa addini shike jan sallah anan kofar gidan tun daga kamsus salawati har zuwa sallar tarawihi. Kuma a lokacin sane aka kafe gidan ta yadda ya gagara gudu ko tawaye, idan mutum ya shiga sai yadda akayi dashi, duk wani ma'aikaci a shekarun 60s70s 80s dayayi suna gidan YARI da bazar YARI MUSA yayita. Allah sarki wani yake fadamin turancinsa SHATAF!!! (Shut up) kuma akwai shi da sarar cewa yanzu nasa a kasarmani kai sama-sama.
Haka YARI MUSA yayi zamanin sa cikin girma da arziki ana shakkarsa babu mai haye masa domin kowa tsoron sa yakeji, bana mantawa idan babana suka gamu da Malam Alasan Dashe Dan sarkin Daura Abdurrahama sai yacewa babana "Ibrahim zamani yacimu da a garin nan da babana da kakanka sai abin da suka fadi babu mai canza musu amma yanzu munzama yan kallo" kuma mahaifina yana fadamin cewa idan sarkin Daura Abdurrahaman zaya Rogogo har gidan YARI yake zuwa da kansa ya karbi sako yakaiwa Kakana Abdullahi dayake zaune can. Haka kuma da sallah motar sarki ake dauka aje Rogogo a dauko jikokin YARI MUSA akawo su DAURA sallah wannan labari duk iyayenmu suke fadamin. Na kumaji wani daga bakin mutanen gari da tsaffin ma'aikatan gidan YARI, a haka aka tafi lokaci mai tsawo kimanin shekara ashirin da biyar ko kusa da haka.
A tsakiyar shekarun 1950s sai ALLAH ya azurta YARI MUSA da zuwa aikin hajji, yaje ya sauke farali ya dawo, bayan dawowarsa sai yace zai ajiye aiki, turawa da masarauta sukace ya bari ya kara lokaci, shi kuma yace a'ah! Tunda yaje makka ya tuba daga duk wani laifi dayakejin ya aikata ba zai sake yin aiki ba, haka sukayi takaddama akace Idan bai kara shekaruba, baza'a bashi fansho ba yace saidai kada a bashi, nasamu labarin cewa ya maidawa Wanda yafadamasa haka martani dacewa kaima kana da bukata kuma insha allah bazata biyaba, "haka akayi kuwa wannan mutum da bakin cikin rasa samun biyan bukatarsa yabar duniya" Daga nan ya ajiye aiki wajan 1955-58 ban samu takaimaiman lokacin ba. Abin bakin ciki na Tarar da akwati guda na takardun aikinsa a dakin nahaifiyata sakamakon shi yariki mahaifina, a hannusa ya rasu amma yarinta da rashin Sani yasa na lalatasu nayi kaca-kaca dasu a farkon shekarun 1980s amma har yanzu nakan iya tuno yanayin rubutun da kuma wasu maganganu dake cikin takardun aikin nasa.
YARI NA MADINA.
Bayan YARI MUSA ya ajiye aiki ba fansho, sai ya dawo gidansa na unguwar garake dake nan tsakiyar birnin Daura inda ya Gina lokacin yana aiki, wato inda aka haifeni kuma muke zaune yanzu nida iyayena, dayake ya saba da gwagwarmaya zuciyarsa bata mutuba, sai yakoma Gona yaci gaba da tsare mutuncinsa Wanda yake bibiyarmu har yanzu mu ba yaran kowa bane zaman kanmu muke mun gwammace muyi wahala wadda zata fishshemu. Alkahu Akbar mutuwa rigar kowa A farkon shekarar 1973 a lokacin YARI MUSA Nada kusan shekara Dari a duniya, Ranar wata lahadi bayan sallar la'asar Allah yayiwa YARI MUSA rasuwa yanzu kimanin shekara arba'in da bakwai kenan a lokacin wata goma kafin inzo duniya. Bayan haihuwata akasamin sunan sa inda na zama MUSA MAGAJIN MUSA. ALLAH JIKAN YARIN DAURA MUSA da sauran abokan aikinsa da kuma al'ummar musulmi Wanda suka rigamu da imani.
A lokacin da YARI MUSA zai ajiye aiki sai mutane sukayo caaa!!! Kowa nason mukamin YARI akayita rubuto takardu, to a lokacin ALHAJI NAMADINA SHINE MALAMIN YARI SHI YASAN YADDA AKE GUDANAR DA AIKIN, DON haka YARI MUSA yace ba Wanda za'aba wannan aiki sai NAMADINA domin shiyasan aikin sai aka ba YARI NAMADINA WANNAN MATSAYI Yazama YARIN DAURA na biyu, yakama aiki kafin samun yan'cin kai har zuwa bayan yan'ncin kai inda shima yayi ritaya a shekarun 1970s zuwa farkon 80s. Daga nan kuma sai aka koma CHIEF WARDER GRADE 1. INDA AKABA CHIEF SULE, A haka aka gangaro har zuwa yanzu danake wannan rubutun, inda yanzu ALASAN YAKUBU DANDO YAKE A MATSAYIN CHIEF WARDERS. SHIYASA NAKE ROKON GWAMNATIN TARAYYA DATA TAIMAKA YADDA AKASAWA BABBAN OFISHIN YAN SANDA NA KASA SUNAN LOUIS EDET SHUGABAN YAN SANDA NA FARKO (IG LOUIS EDET) HAKA KUMA GWAMNATIN JAHA TAMAIDA DAKIN KARATU NA DAURA SUNAN WAZIRI ALASAN A MATSAYINSA NA FARKON WANDA YA KARFAFA BOKO A DAURA SHIMA YARI MUSA A TAIMAKA A GIRMAMA SUNANSA TA YADDA TARIHI BAZAI MANCE DASHI BA. INA KUMA FATAN KUNGIYAR DAURA RORUM ZASU TAIMAKA WAJAN TABBATUWAR WANNAN KAMARI, MUSAMMAN WASU DAGA CIKIN YAN KUNGIYAR SUN SAN WANENEN YARI MUSA. Allahu Akbar tarihi mai raya gida, gari da alkarya Wanda baisan tarihi ba bai San asalinsa ba. ALLAH KASA WANNAN ROKONAWA YASAMU AMSUWA.
MUSA IBRAHIM DAURA
15-12-2019.

Tags:
Daga marubata