Tare da Muhammad Jiddah Nguru
- Malam! Idan aka tambaye ka su wanene 'Yan ta'adda? amsar da zaka bayar babu Mai-maici ko tan-tama, itace: "Hakikanin tantagaryar ‘yan ta’adda sune Wadanda suka tsara kuma suka kaddamar da Kisan Kiyashi akan fararen hula Wanda basu dauke da ko da allura a Matsayin Makami a garin Zariya inda suka kashe 'Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) sama da Mutum 1000
- 'Yan ta'adda Sune: "Wadanda suka je gidan Sheik Zakzaky suka kashe Kananan Yara da jarirai da tsofi da samari da 'yan mata.
- 'Yan ta'adda Sune: "Wadanda suka kashe Dalibai Wanda suke Matakin karshe na kammala jami'a".
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka kashe 'Yan uwa da dama a garin Kaduna, kano, da bauchi sokoto, azare, Potiskum, Funtu'a, da kuma babban birnin tarayya Abuja, kuma har Yanzu ba su daina kashe almajiren Sheik Zakzaky ba".
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka wulla Yaro Mai rarrafe cikin wuta bayan sun kashe Mahaifiyarsa"
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka tona babban rami suka binne Mutane Masu rai da Marasa rai duk suka hada suka binne kuma suka sanya mota tabi ta kan ramin ta dandabe shi".'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka tattaka Mutane da ransu da Motar Soja mai kaca akan kwalta".
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka farka cikin Mace mai ciki da Wuka, Suka barta kwance cikin jini har ta cika bayan jininta ya tsiyaye".
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suke fasa kwakwalwar bayin Allah da bindiga, ko su harbi saitin zuciyar Mutum Yadda babu Yadda za ayi ka rayu.
- 'Yan ta'adda Sune: "Masu Murna ko goyon bayan Wannan Mummunan ta'addaci da aka yiwa 'yan uwa Musulmi kuma tantagaryar azzalumai ne".
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka Jagoranci Sojoji Suka dira a kan jogoran Shiriya Sayyid Zakzaky (H) inda Sojojin Nigeria 'yan ina da kisa suka yi Masa Mummunan harbi a jikinsa".
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka kona Mutane kurmus da ransu, suka yiwa Mata fyade, suka yi dabbancin da ko dabbobi ba sayin irinsa.
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka rushe gidan Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci Sayyid Zakzaky (H), kuma suka harbi duk Masu basa kariya, harbi ne wanda bai Misaltuwa.
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka Kama Sayyid (H) cikin jini da raunukan harsasai da suka harbeshi dasu, har izuwa Yau dinnan yana cikin Mawuyacin halin rashin lafiya baya samun kulawa".
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka bijirewa umarnin da kotu ta bayar na a saki Sayyid Zakzaky Sannan a biyasa diyya amma wannan daqiqir gwamnatin akan ta saki sayyid (H) da Almajiransa ta kuma biya shi diyyar sai tayi biris da wannan umarnin na kotu, kuma ta cigaba da kashe Al-Majiransa".
- 'Yan ta'adda Sune: "Wadanda suka rushe Hussainiyya Baqiyatullah, wuri ne da ake Shayar da ruhin bayan Allah Madarar Soyayyar Allah da Manzonsa da Ahlul-bait (as)".
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka rushe Jannatu Darul-Rahama, Wuri ne da ake binne jikkunan zababbun bayin Allah wato Shahidai, Wanda suka bayar da jinanensu Mai tsarki Saboda neman yardar Allah ta'ala, Darul-rahama wuri ne da ake raya shi da zakirin Allah ta'ala, wuri ne na Musamman da bayin Allah suke shiga halwa na tsawon lokuta.
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka rushe Kabarin Mahaifiyar Sayyid Zakzaky (H). Mahifiyar Sayyid Zakzaky (H) bata yi musu laifin komai, baiwar ce Wadda ta rayu cikin bautar Allah ta'ala, bayin Allah suna ziyartar Makwancin nata suna yin addu'o'i na Musamman ga Wannan babbar baiwar Allah".
- 'Yan ta'adda Sune: "Suka rushe Fudiyya Islamic center zaria, wuri ne da Sayyid Zakzaky (H) yake bayar da karatu ga Manyan Al-Majiransa, wuri ne da ake yin tarukan Munasabobi daban-daban na addinin Musulunci
- 'Yan ta'adda Sune: "Wanda suka rushe gidan Harisawa. gida ne da Masu bada tsaro da tsari a tarurrukan harka Islamiyya suke kwana, gida ne da ake tarbiyyar ruhin bayin Allah.
- To wallahi Tallahi Munanan Muna muku Mummunar addu'a, kuma tabbas zamu rama.
- Ya Allah Muna rokonka dan sirrin dake tsakaninka da Manzonka da Iyalan gidansa tsarkaka (as) Ya Allah ka cikawa Sayyid Zakzaky (H) burinsa na ganin addininka ya tafi da iko a Wannan kasa tamu Nijeriya da ma duniya baki daya.
- Ya Allah ka bawa Sayyid Zakzaky lafiya, Allah ka kunyata Makiyansa bihakki Muhammad Wa ahli Muhammad.
Tags:
Tunatarwa