Sau tari mutane kan dauka samun 'yancishine bawa ya zama an bashi aminci, ko kuna wanda ake tsare wa ya zam sakakke. To, hakika wannan wani sashi ne na 'yanci amma sanin ainihin menene 'yanci sai mun dangana da gidan da basa karya, wadanda akai duniya da lahira domin su.
Imam Al-Sadiq (As) yace; "Akwai wasu siffofi guda biyar duk wanda bai mallaki daya daga cikin su ba, to shi ba abin sha'awa bane. Gasu kamar haka: Biyayya, fushi mai kyau, tawali'u gungiyar hadin kai. sai kuma wanda ya hada dukkan su shine; 'yanci."
Imam Ali (As) yake cewa; "hakika Annabi Adam bai samar da mace ko namiji ba, don haka dukkan mutane 'yantattu ne."
Imam Ali (As) ya kara cewa; "Kada ka yarda ka zama bawan wani, bayan Allah madaukakin sarki ya yika mai 'yanci."
Imam Ali (As) bai gushe ba yana cewa; "Ko wanni abin halitta 'yantacce ne kamar yadda yazo a halittar ko wanne. Mutum mai 'yanci kuma bawa ne, matukar ya zama marowaci.
Sharhi
Idan muka duba wannan hadisin na karshe dakyau, zamu ga azzaluman nan dukkan su bayi ne, domin marowa ta ne da bala'in son handama. Bugu da Kari su azzalumai ne masu zaluntar raunana.
Mutumin da yazam mai rowa tabbas zai iya yin komi don yaga yayi rowa din hakan kuwa koda kisan kai ne, kuma munga hakan domin wannan shine aikin da suka fi aikatawa don biyan bukatunsu da cika muradan kansu. Hakika mu masu 'yanci ne tunda muka fahimci kiran mai jaddada kalmar Allah, domin yanci yana samuwa ne ga wadanda suka 'yantu da 'yantawar Allah, tare da aikata kyawawa. Alhamdulillah muna godiya gareka ya Allah daka fahimtar damu hanyar nemawa bayinka 'yanci.
Ya Allah kaine gatan mu kasan damuwoyin mu ka iya mana akan wadannan azzalumai, domin bamu da karfi sai naka, bamu da kowa saikai.
Wasallallahu ala Muhammad wa alihid daahireen..
Bin Haroun Sigau
08065008703
Tags:
Tunatarwa