Ruwan da akan bawa mutane, su zam 'yan Shi'a!!!


Sanin kowa ne Shi'a wata mazhaba ce dake biyayya ga iyalan Manzon Allah (S) da bin koyarwar su na hakika. Hakan yasa daka Ambaci Ali, Fatima, Hasan, Husain saika ji ana wannan ko shima dan Shi'a ne??

Wasu masu dungurarriyar fahimta ma cewa suke ai yan Shi'a ruwan rubutu suke bawa mutane su zama yan 'yan Shi'a, to, yakai wawa jahili maras ilimi kana ganin inda wannan maganar taka gaskiya ce kai kanka bazamu shi'antar dakai bane?

Wallahi da yan Shi'a wani abu ke bawa mutane su Shi'antu abin nan kuwa kudi ne, ruwa, ko kadara, to da duk duniya yanzun ba abinda ya saura na wadanda ba shi'a ba. Amma ita ainihin fahimtar shi'a zabi ne daga Allah (T), da kuma son gaskiya komi dacin ta.

Tabbas akwai ruwan da ake bawa kutane su shi'antu, amma ba kamar yadda kuke tunani bane. Ruwan shine tsantsagwaron shayar da mutane gaskiya, da nuna musu ita a aikace.

Da yawan Malaman wasu mazhabobi zaka gan sun bambanta dana shi'a. Me yasa nace haka?? Zaka ga malami masani amma yafi kowa aikata badala da ruguje koyarwar Annabi (S), taya kuke tsammanin mai aikata sabo zai karbi gaskiya a wajen abokin badalar sa?

Wannan shine abinda ya haifar da rashin yawar musulunta kafirai a wannan zamani, domin kaine zaku je gidan mata, gidan rawa, gidan giya, gudan dukkan wata alfasha tare da kafiri kuma kace masa wai kana kan hanyar daidai ya saurare ka?

Addini aiki ne shiyasa kyawawan dabi'un Manzon Alkah suka kaishi gayin nasara muma ta wannan hanya mu kesa mutane su fahimce mu, suyi sha'awar kasance wa kamar mu. Mu ba kira muke da kudi ko bada rubutun sha ba, a'ah kira mu da aiki da gabbai ne. Domin wannan tafiya saima dai, kai kake bayarwa bawai a baka ba.

'Yan uwa mu kara dagewa da sadaukar da lokacin mu wajen bautar Allah kada mu bari shaidan yake galaba wajen lalata akhlaq din mu, kullum muzam masu yiwa kanmu hisabi. Idan muka lizimci haka sai ya zam mun tsinkayi kawukanmu da samun rabo mai girma duniya da lahira.

Allah ya datar damu, ya azurta mu da arzikin da muka fi bukata yanzu na yi mana tagomashi da fitowar su Sayyid Zakzaky (H). Albarka cin Ma'asumah Fatima (Sa).

🇳🇬 Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bin Haroun Sigau.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post