-Sayyid Mustapha Lawan Nasidi Potiskum,
Wanda ya tsanan ta qwanqwasa qofa, wata rana zai shiga. Idan mutum ya je gidan mutane sunyi bacci, ya dinga buga qofa, gwan gwan gwan, baza a kai wani lokaci da za su ji, su farka ba? To Allah ba bacci yake ba, yana son ya ga gaskiyar zuciyar bawa ne, dagaske ne yana so ya shigo, a bude masa qofa? In yana so ya shigo, to ya gaskata, yayi ta qwanqwasa kofar, yayi ta qwanqwasawa. Yaya ake qwanqwasa qofar? A bar zunubi, kar ayi sa6o, kar a ci haram, kar a cika ciki, kar a kwana ana bacci, kar a daina karatun alqur’ani, haka za ayi ta yi, har a kai ga samun yardar Allah (T).
-Sayyid Mustapha Lawan Nasidi Potiskum, wani bangare na jawabin da ya gabatar a Mu'utamar din da aka gabatar a garin Lafiya ta jihar Nasarawa.
*-El-Tafseer*
Tags:
Jawaban Malamai