* BABU GWAMNATI SAI TA ALLAH!
* bindiga da mabudin arziki kawai Bazzalumai suke da.
* HAR ABADA BA ZA MU YI MUSU BIYAYYA BA!
- Cewar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bayan fitowa daga kurkukun Abacha a 1999.
JAWABIN MALAM ZAKZAKY YAYIN DA YA ZIYARCI MAKABARTAN WADANDA ABACHA YA KASHE BAYAN FITOWARSA DAGA KURKUKUN ABACAN
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
“Dama makasudin zuwanmu nan ba shine jawabi ba, mun zo ziyara ne na ‘yan uwanmu wadanda suka cika alkawari (wadanda sukai shahada), mu ziyarce su, mu yi musu addu’a, sannan mu roki Allah ga kawukanmu albarkacinsu kafin mu wuce. Wani lokaci insha Allahu ta yiwu a yi jawabi, amma yanzu insha Allahu addu’o’I ne za mu yi mu wuce. Kuma dai har ma mun riga mun yi addu’o’I da ziyara din tun kafin a mika abin Magana.
“Wannan wata alama ce akan hanya, wato in kana tafiya zuwa wani wuri, akwai wasu alamomi da sukan nusassheka cewa hanyar da kake bi ita ce hanyar da za ta kai ka wurin da za ka. To wannan alama ce babba cikin alamomi na tafiya a tafarkin Allah (T). Kuma Allah (T) ya yi mana jarabawa wadda (ko da yake har yanzu bata kare ba), amma wannan marra ta kamar shekara 2, wanda yake amma kafin wannan lokacin ba mu gamu da jarabawa kamar irinta ba.
“A lokacin da nake jin labarin abubuwan da suke faruwa, nake gaya ma wanda nake da sila das u a wannan lokacin cewa abubuwan da suka faru, ni ba su bani mamaki ba. Amma na yi mamakin zuwansu da gaggawa. To amma tana iya yiwuwa wata alama ce tacewa nasara ma ta kusa zuwa da gaggawa ne.
“Tabbas an jarabamu. Kuma wadanda suka jaraba din, sun yi iyakan kokarinsu suga cewa mun gaza. Na farko sun dauka dai idan suka bude wuta kowa zai san inda ya nufa. To waki’ar nan sai ta karyata su. Sai suka bude duk irin wutan da suke iya budewa, sai jama’a sai bumbuntowa suke yi. Kuma ba su ga ko gezau wani ya yi ba.
“To wannan yasa su a kansu sun san cewa jarabawa dai kam an riga an ci. Kuma lallai an yi kokawa. Kuma lallai mu makai kaye da karfin Allah!
“Nasha jin wasu suna cewa wai ba wanda ya fi karfin gwamnati. To mun fi karfinta! Lallai in kace su waye suka fi karfin gwamnati, ga mu! Domin gwamnatin, gwamnatin IBLIS ce. Mu kuwa abin da muke cewa BABU GWAMNATI SAI TA ALLAH! To yaya kuwa gwamnatin Iblis za ta bamu tsoro?
“Iyakan abin da suke da su kenan abubuwa biyu; bindiga da mabudin arziki. Bindiga ba kayansu bane ba kayan Ubansu bane! Bindiga din ta al’umma ce. Al’umma ce ke da bindiga. Kuma arzikin kasa da suka rike mabudan suke tatsowa suke azurta kawukansu suke taskacewa suma arzikin al’umma ne. saboda haka mun san da bindigar, da kuma arzikin da suke tatsa duk kayan al’umma ne da Allah (T) ya azurta ta da su, amma ba kayansu bane.
“Saboda haka, Ta yaya ne, wanda ya rike kayan da ba nasa ba, barawo, azzalumi, zai dauka cewa wai shi zai iya bad a tsoro. To iyakanta kenan, ya yi amfani da abin da yake iyawa; Bindiga ya yi harbi, ba shikenan ba? Ya kuma gama. Kurkuku kuma ya kai. Amma bashi da Jahannama.
“Wannan kuma waki’a lallai kam Alhamdulillahi, ga wadanda aka jaraba, sawa’un wanda sukai kurkuku ne, ko wadanda suke waje, duk ba wanda ya gaza a cin wannan jarabawa.
“Na waje wadanda su suka fi mu mu na ciki, su sun gwada a zahiran, sun gasgatawa Allah alkawarin nan da sukai masa. Inda aka bude wuta, kuma ba a samu wani ya ja baya ba. Ballantana kuma mu da suka dauka irin tsarewan da sukai mana suka takuramu, tana iya yiwuwa (irin abin da Hausawa ke cewa a Karin Magana; Idan ruwa na cin mutum ko takobi wai ka ba shi zai kama). To said a suka saka mu a irin wannan halin, sai suka miko takobi, sai muka hararesu, suka miko igiya aka ki amsa, suka miko duk abin da za su iya, mukace ba bukata. Muka ce in dai wannan ne, ku cigaba. Karshe kuma ya zama dole-dole ko mutum ya so ko yaki gaskiya ne sun yi saranda ne! kuma wannan karamin saranda ne, da sannu babban saranda na nan tafe, inda Allah (T) zai tabbatar da addininsa a doron kasa.
“Kuma garemu, kar mu dauka karshen jarabawa kenan. In ba a manta bat un farkon wannan al’amari sun ta jarabawowi iri-iri. Kamu da dauri – kamu da dauri, akai tat a yi. To wannan karon ne suka gwada kisa. Kuma da suka ga sun yi kisan, shima duk wannan bai kai ba, har sai suka fara keta alfarma da cin mutunci, da cin zarafin mata da yara. Tsammaninsu cewa za su iya harzukamu har mu zama mahauka kamar su.
“Amma sai ya zama a zahiri Duniya tai shaida, fada ne aka yi tsakanin mahaukata da masu hankali, suka nuna ma Duniya gaba daya sune mahaukata. Kuma mun nuna ma Duniya gaba daya muna da hankali, mun san abin da muke yi. Kuma tsonarasu bata sa mun murza hankulanmu ba, muna nan daram akan abin da muka tsaya akai.
“Addini na Allah ne. mun tabbatar da cewa kasar nan da muke zaune a ciki, Allah (T) ne ya halicceta. Kuma mu din nan da muke dore akan wannan kasar Allah ne ya haliccemu. Arzikin da ke birbishin kasan nan Allah ne ya yi. Wadannan mutanen da suke rike da iko, ba su yi halitta ba, ba kuma sa azurta halitta. Kuma mun tabbatar da cewa Allah (T) Mahaliccin sama da kasa ya aiko da ManzonSa da sako, sakon nan shine Musulunci, kuma Musuluncin nan yana nan. Kuma mun tabbatar wadannan mutane ba Musuluncin suke ba. Saboda haka ba batun har abada ko me za su yi kan cewa za mu yi musu biyayya.
BABU GWAMNATI! SAI TA ALLAH!
“Rokonmu ga Allah (T) ya azurta wadannan bayin naSa da aka karkashe a waki’o’I daban daban, da karbansu a matsayin Shahidai. Ya yafe musu, ya yafe ma iyayensu, da yayan da suka bari a baya, da zuriyansu da iyalansu, ya kuma karbi ayyukansu, ya riskar das u da rayayyu wadanda yake azurtawa. Kuma yasa jinainansu su zama tamkar abin da zai bada ruwa ga itaciyar tabbatan addini Insha Allahu.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
_______________
Saifullahi M. Kabir ya rubuto muku daga audio din jawabin.
