KISAN KARE DANGI


A wani rahoto da aka taba fitarwa akan kisan kiyashin da haramtacciyar kasar isra'ila keyi akan palastinawa ya nuna cewar ya zuwa wancan lokacin da rahoton ya fita akwai iyalai Sama da 25 Wanda gaba daya an shafe su a doron kasa ba da ba jika ba iyaye ba kakanni gidajen sai dai a rufe in har ita HKI bata riga ta ruguza gidan ba kenan, a wani abu mai kama da arashi a harinda sojojin Buhari da buratai 'yan ina da kisa suka kawo wa harkar musulunci a nijeriya a ranar 12/12/2015 a Cikin awanni 48 sunyi barna a Cikin iyalai da da dama inda suka kusan karar da wasu wasu saura kalilan, abun kamar da gayya da kuma daukar hannu na irin mugun aikin iyayen gidansu Amurka,isra'ila da saudiyya idan kayi laakari da irin ta'addancin da suke tabkawa a palastinu,siriya,iraqi,afghanistan da Yemen.zakaga kwabo da kwabo aikin iri daya ne burinsu su halaka duk iyalai tare da rusa al'umma baki daya,wadannan hotunan da kake gani tsarine na iyalai da sojojin nijeriya suka kashe baki daya a zariya kuma ma ba suke nan ba akwai wasu ma da ban kai ga hadawa ba,dame zaka kwatanta irin wannan baqin hali na sojojin nijeriya bisa jagorancin buratai da Buhari.

yakamata sauran al'umma su Sani suma fa suna da iyali,ya zasu kwatanta kansu idan irin haka ta faru dasu,lokaci yayi da al'umma zasu farga su gane cewa waqi'ar nan fa ta shafi al'umma ne baki daya ba wasu jinsi na da ban ba, idan kuwa kana ganin abun a haka to kayi wawanci,na tabbatar randa irin haka ta same ka zaka so ka sami masu tausaya maka Alhali ka makara kabar shiri tun Rani kuma ka fafe gora ranar tafiya,yakamata ku Sani maqiyanmu fa sune maqiyanku kuma maqiyan al'umma baki daya in yau sun dirar mana gobe kuma fa? in sun kashe shi'a a nijeriya da Iraqi to a palastinu da Afghanistan wa suke kashewa? kayi tunani mana yakai mai dariya,ko kana ganin ka tsira ne? kukan kurciya.....

Wallahi Tallahi ko kaffara babu da a ce wasu akayi ma abinda akayi mana, musulmi ko kirista kai indai bil adama ne, kuma Malam zakzaky na nan a raye, to bazai taba goyon bayan azzalumai ba, zai kasance ne tare da wadanda aka zalunta kuma iya karfinsa zaiyi bazai taba shiru ba, kuma kaima kasan hakane,ko akwai mai musu?

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post