Ma'asumah Nigerian News Updates.
A yau Lahadi 10/11/2019 yan uwa musulmi masoya Manzon Allah (S) na Da'irar Saminaka suka gudanar da gagarumar Muzaharar Mauludi a cikin garin na Saminaka.
Jirgin muzaharar ya fara ne daga bakin kasuwa. Inda a nufi hanyar gidan Sarkin garin na Saminaka. Dubbannin Yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky (H) ne da kuma mabiya Darikar Tijjaniya suka hau kan kwalta a yau din domin gudanar da Muzaharar cikin lumana.
Muzagarar ta bana tazo da salo kala daban-daban, kuma ya isar da sako ga al'umma sosai. Wakilin yan uwa na Da'irar ta Saminaka wato Malam Yusuf Abubakar shine ya rufe muzaharar a cikin babban tasha dake garin. An kammala lafiya kamar yanda a fara lafiya.
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- 10/11/2019
Tags:
Munasabobi
