YA RAGE KUƊIN KAYAN SHAGON SA SABODA WATAN MAULUDI

WANI BAWAN ALLAH YA RAGE KUƊIN KAYAN SHAGON SA SABODA WATAN MAULUDI

Wani bawan Allah mai suna Sayyadi Usman Muhammad (Sufi) ya rubuta cewa ya rage kayan shagon sa saboda shigowar watan Mauludi wato watan da aka haifi Annabi Muhammad (SAW).

Usman Muhammad wanda mazauni ne a cikin garin Gombe yana da shagon saida kayan masarufi a cikin babban kasuwar Kumo.

Ya ƙara da cewa ya yi hakan ne don nuna farin cikin sa da wannan wata da kuma baiyana soyayya ga fiyayye halitta Annabi Muhammad.

Allah ya sa sauran yan'kasuwa suyi kori dashi don saukake wa al'umma wahalar da suke ciki

Allah ya ƙara masa arziki sa. Amiin

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post