TARON TUNAWA DA WAKI'AR MAULUD (12/12/2015) A GARIN DAURA



A yau Alhamis ne Dandalin Matasa karkashin jagarancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Daura da kewaye, sun gudanar da _Zikirah_ na waki'ar Zaria.
Bayan bude taro da addu'a da karatun Alkur'ani mai girma. Dalibai yan fodiyya sun yi Faretin girmamawa ga Shahidai, tare da daga hotunan shahidan yankin Daura.
Shaheed Nafiu Musa Daura.
Shaheed Abubakar Musa Rimin guza.
Shaheed Umar Isah Tela Daura
Shaheed Salahuddeen Auwal Daura
Shaheed Yusuf Sulaiman Art Daura.
Dukkansu sun samu shahada ne a Gyallesu, wajen ba da kariya ga Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
Wakilin Yan uwa na garin Daura Malam Mustapha Muhammad ne ya yi Jawabi a wajen taron.
Taron ya samu halartar yan uwa da dama a sassan yankin.
A ranar 12/12/2015 ne Sojojin Nigeria suka Qaddamar da hare-haren ta'addanci a kan yan uwa Musulmi a garin Zaria, inda suka fara bude wuta a kan yan uwan da ke Husainiyya Bakiyyatullah, da Gyallesu gidan jagoran Harka Islamiyya da kuma Darur-rahma dake Dembo Zaria, duk da sunan an tarewa Burtai hanya. Inda suka kashe yan uwa sama da 1000 tare da harbe Jagoran Harka Islamiyya Shaikh Zakzaky (H) da kuma ci gaba da tsare dashi da Matarsa Malama Zeehat da sauran yan uwa. Duk da kotu ta bayar da umurnin a sake su.
📷




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post