TARIHINTA {SAYYIDA ZAHRA}


______Jibril Usman Sarki
An haifi Sayyida Fatim a (AS) a Makka, ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Sani, Shekara ta biyar, bayan aiko wa Manzon Allah (S) da sa}o. Akwai sashen Malamai da suka tafi a kan cewa she}ara biyu bayan bi’isa ne. Amma su Malaman Ahlus Sunna sun tafi a kan cewa she}ara biyar gabanin aiko Manzon Allah (S) ne aka haife ta. Sunan Mahaifiyarta, kamar yadda aka sani, Khadijah (AS). Tana da shekara biyar Allah (T) ya yi wa Mahaifiyarta rasuwa, domin ta rasu shekara 10 bayan bi’isa. Har ila yau a wannan shekarar ce Allah (T) ya yi wa Abu [alib (AS) rasuwa.

Ya zo a kan cewa tsakanin rasuwar Khadija da Abu [alib (AS) kwana uku ne. Shi ya sa shekarar aka yi mata la}abi da shekarar ba}in ciki. Bayan rasuwarsu ne Manzon Allah (S) ya tafi [a’ifa domin isar da sa}.
Wani dan tambihi a nan shi ne, Malaman Madrasah ]in Ahlul Baiti (AS) sun tafi a kan cewa ’ya’yan Manzon Allah (S) baki ]aya an haife su ne gabanin aiko masa da sa}o, in ban da Sayyida Fatima (AS) da kuma Ibrahim ]an Mariya. Su bayan bi’isa ne aka haife su. Har ila yau akwai ayyukan da ake son aikatawa ranar wiladar Sayyida Fa]ima (AS), daga ciki akwai Azumi, wato ana son mutum ya yi Azumi a ranar domin godiya ga Allah (T) ga wannan babbar kyauta da ya bayar, da kuma yin Alhairai a ranar da sadakoki ga muminai da kuma yin ziyara ga Sayyida Fa]ima (AS).

Yadda ziyarar take, mutum na iya komawa ga littafin Mafatihu. Har ila yau a irin wannan ranar ne ta haihuwar Sayyida Zahra (AS) aka haifi Imam Khumaini, an haife shi ne 20 ga watan Jimada Sani a she}ara ta 1321 bayan hijira.

Sayyida Fatima (AS) tana da sunaye da yawa da kuma la}ubba masu yawa. Imam Sadi} (AS) ya ce Fatima (AS) tana da sunaye tara a wajen Allah (T), su ne: Fatima, Siddi}a, Mubaraka, [ahira, Zakiyya, Radiyyah, Muhaddisa da kuma Zahra. A wata ruwaya, akwai Mardiyya, da kuma Batul. Daga kuma cikin la}ubbanta, akwai Ma’asumma, Karima, Shahida, Rashida, Sabira, Mu’azzama Mazluma da dai sauransu. Haka nan kuma tana da kinaya da yawa, amma wa]anda suka fi fice su ne: Ummul A’imma da kuma Ummu Abiha.

Ya zo a kan cewa Manzon Allah (S) ne ya yi mata kinaya da haka. Manzon Allah (S) ya kasance yana girmama Sayyida Fatima (AS) gayar girmamawa. Ya zo a kan cewa in ta zo wajen shi a gida yakan tashi, ya ce ta zauna inda yake zaune. Haka nan Manzon Allah (S) ya kasance idan zai yi tafiya, bayan ya bar gida, sai ya biya wajen Sayyida Fatima (AS) ya yi bankwana da ita, sannan ya tafi, in kuma ya dawo daga tafiyar, sai ya biyo gidan Fatima (AS), sannan ya wuce gida.

Sayyida Zahra (AS) ta tashi a Makka, gaban Mahaifinta. Saboda haka dukkan tsangwama da wahalhalu da Manzon Allah (S) ya fuskanta daga ma}iya a Makka wajen isar da wannan sa}o, a gaban idonta suka wakana. Ya ma zo a tarihinta cewa, bayan rasuwar Mahaifiyarta Khadija (AS), idan Manzon Allah (S) ya fita yin da’awa, kuma ma}iya suka yi masa jina-jina, in har ya dawo gida, Sayyida Fatima (AS) ce ke wanke masa. Akwai lokacin da ya je Ka’aba yana Salla, bayan ya yi sujuda ma}iya suka ]auko tumbin dabba, wanda ya ru~e yana wari suka sa masa a baya. Sai aka je aka shaida wa Sayyida Zahra (AS) ita ta zo ta ]auke masa. Daga irin wa]annan ayyuka da take yi wa Manzon Allah (S), wasu Malamai suke ganin wannan kinaya da Manzon Allah (S) yake yi mata na Ummu Abiha ya samo asali. Haka wannan yanayi ya ci gaba da gudana har zuwa lokacin da Manzon Allah (S) ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina.

Kafin hijirarsa, ya yi umurni ga Imam Ali (AS) da ya kwana a shimfi]arsa, da kuma mi}a masu ajiyoyi da amanonin kayyayakinsu. Bayan nan ya zo Madina ya same shi tare da iyalinsa. Haka kuma al’amarin ya auku bayan Imam Ali (AS) ya mi}a amanoni da kuma ajiyoyi na mutane, sai ya kama hanya zuwa Madina tare da wa]annan bayin Allah (T), su ne Sayyida Fatima (AS) da Fatima ’yar Asad, wato Mahaifiyar Imam Ali (AS), da Fatima ’yar Hamza, da kuma Fatima ’yar Zubair ]an Abdul Mu]allib, tare kuma da wasu mazaje guda biyu, su ne Ai’man da kuma wani da ake ce wa, Abu Wa}idil-laisi. Haka suka yi hijira daga Makka zuwa Madina, suka bar Makka da rana, ido na ganin ido suka kama hanya.

Bayan fitarsu, sai {uraishawa suka aiko maya}a takwas a kan su bi su da umurnin cewa su kashe Imam Ali (AS). Suka bi su, suka same su a wani waje da ake ce wa Dajanan. Da Imam Ali (AS) ya ga haka sai ya tsai da tafiyar, ya ce wa wa]annan mazaje guda biyu da ke tare da shi, wato Ai’man da Abu Wa}id, da su gurfanar da ra}uman da wa]annan bayin Allah (T) ke kai, ya sa a ]aure ra}uman. Bayan haka ya tafi wajen su ma}iyan da takobinsa, sa-in-sa ta magana ta gudana a tsakaninsu. Daga cikin abubuwan da suka ce wai shi da wa]annan bayin Allah (T) su koma Makka ]au’an ko karhan. Haka dai musayar maganganu suka gudana. Daga }arshe abin ma ya kai ga gumurzu. Tunda suka ga Imam Ali (AS) ya samu ]ayansu, wanda ya fi za}ewa, ya rafke shi, ya sassare shi da takobi, ganin haka sauran maya}an suka tarwatse suka gudu. Bayan haka sai su Imam Ali (AS) suka ci gaba da tafiya har suka iso Madina.

Ya zo a kan cewa lokacin da Manzon Allah (S) ya iso Madina, bai shiga Madina ba. Ya tsaya a wani waje ne da ake ce masa }uba, har a lokacin wasu suka ce masa ya shiga Madina mana, ya ce, ba zai shiga ba har sai ]an Amminsa da kuma ’yarsa sun iso, haka kuwa aka yi. Sai da suka iso, sannan Manzon Allah (S) ya shiga Madina. An ce lokacin da Imam Ali (AS) ya iso Madina }afafuwansa sun kukkumbura sun kuma tsattsage, saboda ya zo a }asa tun daga Makka har zuwa Madina, ba a kan dabba ba.

Insha Allah a kashi na biyu na darussa daga rayuwar Ummul A’imma, Fatima (AS) za a ]ora a kai. Wato rayuwar Sayyida Fatima (AS) bayan komawa Madina.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post