Matsayi da sanin ainihin wacece mace a Musulunci




A cikin Qurani, Allah mai girma da daukaka ya rarraba wa maza da mata ayyukansu da yanayin da zasuyi tarayya bai ware ko guda ba (mace ko mamiji).

Allah ya haskaka mana hasken sa ta hanyar raba mana jinsi a cikin halittun sa. Ya kuma nuna mana hanyar da zamu kare kanmu da kuma yadda zamuyi rayuwa a cikin al'ummar mu.

Allah yana cewa cikin AlQurani mai girma: "Ya halicce ku daga rai guda, kana ya samar masa  abokiyar  tarayya daka jikinsa"

"Shine ubangijin sammai da kassai, kuma ya samar daga gareku, abokan tarayya. A cikin dabbobi ma yai musu abokan tarayya, sa'an nan ya rubanya ku. Don haka shine wanda babu kamar sa, shi mai ji ne, kuma mai gani ne".

Kuma ya fada cewa; "Yaku 'yan Adam! Kuji tsoron Allah ubangijin ku, wanda yayi ku daga gudan jini, sannan yayi ku maza da mata ya warwatsa ku daga ko wannen ku maza da mata, kuma da izinin sa ne ya halitta daga gareku abokan tarayyan ku domin ku sami natsuwa daga garesu. Sannan ya sanya muku soyayya da rahama.

Hakika, a cikin hakan akwai alamomi na mutane masu tunani."

Muslunci ne ya koyar damu, mu zama cikin gode wa Allah ga dukkan ni'imomi mara sa qirguwa da yayi mana. Yaci gaba da cewa; "kuma ya sanya ka a cikin mahaifiyarka ba tare da ka san komi ba, ya baka jii, gani, da ilimi wataqil kaa gode masa".

Sabida haka, Muslunci ya muhimmanta da duk wani bayani da ya shafi matsayin mata a cikin al'umma, dangantakar su  da maza ne a matsayin uwaye, matan aure, kannai ko kuma 'ya'ya.

Ya sanya dukkan wata yarjejiniya, hani da umurni domin tabbatar da ta ko wanni bangare mata sun zama cikin kariya da girmamawa cikin al'umma.

βιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
08065008703

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post