A karkashin sharhin Tafsirin aya ta 4 a cikin Suratul Nasi, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cewa:


"Akwai masu cewa yaya ma za a ce akwai wani Ma'asumi ne? "Ma'asumi man asamahullah" Ma'asumi shine katangagge daga laifi.

"To da wata ibara, na taba gani a wasu zantukan Imam Khomeini (QS) yana cewa "Duk mumini Ma'asumi ne a wani mikidari"
"Alal misali, idan kai baka shan Giya, ko da za a sauke ka a masauki, a wani daki da Kwalabe na Giyoyi masu tsada, baza ka sha ba, sam baka sha'awa, zuciyar ka ba ta sawwala maka wannan, to kai Ma'asumi ne dangane da shan Giya. In kana tunanin kai sam baza ka kashe babanka ba, to kai Ma'asumi ne a wajen kashe babanka. Idan kana tunanin kai baza ka kashe danka ba, to kai Ma'asumi ne a wajen kashe danka. Ko Kafiri in har baya tunanin ya kashe ubansa, to shi Ma'asumi ne a wajen kashe ubansa, kaga dai shi Kafiri ne.

"To yadda kake ganin kake iya zama Ma'asumi a wani abu, to haka wasu suke zama Ma'asumai, hatta akan 'yan kananan zunubai, sunfi karfin su aikata. Suna da 'Nafs Ƙawiy', hankalinsu yafi ƙarfin son ransu, komai ƙanƙantarsa, don haka ne suka cancanci yabo.

"Wato 'Nafs' wanda ko kai kanka kana iya ginawa zuwa wani digiri, tun da ko kai kanka kana iya ƙoƙari ka samu Isma a wani digiri, to me yasa kai zakayi mamakin wani ta nan? Ai wani zai fi ka ta nan ko?

"Za ka iya kokari ka zama ka samu isma akan wasu ba'adin kaba'ir, baza kayi su ba. Akwai wasu kaba'ir wanda mutum sam baya tunanin yayi su. Misali mutum baya tunanin zai sha Giya, baya tunanin zai yi kisan kai, baya tunanin zai yi Zina, irin wadannan duk yana tunanin bazai yi ba).

"To amma tanan iya yiyuwa yayi Giba, shima Kabira ne, ko yayi girman kai, ko yayi Hassada su ma kaba'irai ne, to amma ta yiyu wannan sai yayi hobbasa sosai, sannan zaifi karfin, Hubub, Khibir, Hasad da Giba da ire - irensu. To haka kuma yana iya fin karfin Saga'ir, kananan zunubai, alal misali yafi karfin ya kusance su, kuma yana iya barin wasu daga ciki.

"To idan aka ce maka haka nan ne, kai zaka iya yin wannan, to ina kuma ga wasu bayin Allah? Kaga su zasu kai mustawan da ya wuce naka ne ai ko?

"Wani ya taba tambayar Imam Ridha (AS) yace; "Kana nufin ku ba kwa sha'awar zunubi? Ance ku ba kwa sabon Allah." Sai yace masa; "Ka taba ganin tsuguno, yayin da ka tsuguna? (Irin tsuguno da mutum yake yi ta fitar da wani abu). Yace eh! Yace "Ka taba sawwala ka debo ka ci? Yace a'a. Yace masa 'to haka muke kallon zunubi"
"Wato yadda kake kallon tsugunonka baza ka sawwala ka debo ka kai bakin ka ba, haka (Ma'asumai) suke kallon zunubi, ko da dan kankani ne.

"Muna iya cewa babban shedanin ka a ina yake? a zuciyar ka, kaine babban shedanin kanka, in kafi karfin kanka shike nan. Amirulmuminin Imam Ali (AS) yana cewa "Wanda duk bashi da mai wa'azi a ransa, da mai tsawatarwa, to ba zai samu mai wa'azi daga wajen sa ba, komai mai tsawatarwa".
"Wato indai baka tsawatarwa kanka, ka yiwa kanka wa'azi ba, to wa'azin waje ba zai amfane ka ba.

"Alkhannas an kira shi haka nan, saboda yawan yi kenan, waswasi, mai yawan bayyana ya bace, wato ya je ya dawo. Da a ce in kafi karfin sa sau daya an gama, ina! kokawa ne za a dinga bugawa har a mutu, tsakanin ka da son rai."

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post