Shin, Akwai hujja Cikin Aurar da 'yarka ga Ba'ame ???


WANNAN AL'AMARI DA 'DAUREWAR KAI YAKE

Akwai abu da ake kira lalura wanda kan sa ka aikata wani abu wanda bai dace ba a shari'ar muslimci. Sai dai shi wannan abu yakan zama na wani lokaci ne (temporary) ba dawwamamme ba.

Idan muka dauki cin mushe za muga cewa haramun ne, amma wani lokaci yakan zama halas, sai dai halascin nasa kan zama na taqaitaccen lokaci ne wanda daga baya yakan koma kan haramcinsa.

Hakama aikata zina kan zama lalura don neman kubutar da rai, amma shi ma ba zai zama dalili na cigaba da aikata shi ba.

Fahintar gwagwarmaya abu ne wanda mai tsananin rabo ne kadai ke samun sa, shi yasa za kaga wasu sun tara karatu tuli amma fahintar abinda ke cikin karatun ya gagare su, sai wanda kake ganinsa a matsayin marar karatu ya fahinta.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post