Qabilar Quraishawa a Cikin larabawa..!!


SHIMFIDA GA HAIHUWAR MANZON ALLAH (S.A.W.W)

Kafin asan tarihin mutum ya kamata a san tarihin qabilarsa, matsayin kakanninsa a cikin wannan qabila.

Shi dai Muhammad Manzon Allah (S.A.W W) Balarabe ne dan qabilar Quraishawa. Ita kuwa qabilar quraishawa ita ce mafi daukakar qabilar larabawa mafi daraja.

Ana danganta wannan qabila ne zuwa kakan Manzon Allah (S.A.W.W) na goma (10) mai suna Quraishu, wanda aka fi sani da Fihiru Bn Malik.

Shi kuma Fihiru Bn Malik ya kasance mutum ne mai yawan taimakon mabuqata. Wanda yazo da buqatarsa a wajensa ba ya hana shi, idan mai neman tufafi ne ma yazo masa sai ya tufatar da shi. Idan kuma matsoraci ne yazo masa sai ya amintar da shi, wanda kuma ya bace sai ya dora shi akan tafarki madaidaici. Duk Balaraben da nasabarsa bata biyo ta kan Fihiru Bn Malik ba, to, haqiqa ba Baqureshe bane.

       BANU HASHIM

Ita kuma qabilar Banu Hashim sune mafi daukakar qabilun Quraishawa, saboda haka Manzon Allah (S.A.W.W) shine zababben Balarabe kuma zababben cikin qabilun larabawa.

Ya zo cikin hadisi inda Manzon Allah (S.A.W.W) ke cewa;

" HAQIQA ALLAH (S.W.T) YA ZABI ISMA'IL DAGA CIKIN 'YA'YAN IBRAHIM, KUMA YA ZABI KINANATA DAGA 'YA'YAN ISMA'IL, KUMA YA ZABI QURAISHAWA DAGA CIKIN KINANATA, SANNAN YA ZABI BANU HASHIM DAGA CIKIN QURAISHAWA. NI KUMA YA ZABE NI DAGA BANU HASHIM. SABODA HAKA, NI ZABABBEN TSATSO NE MAFI GIRMAN ZABABBUN TSATSON LARABAWA."

Bisa wannan shimfida za mu fahinci cewa kakannin Manzon Allah (S.A.W.W) da iyayen sa sune mafiya daukakar qabilun larabawa, kuma sune mafiya daukakar qabilun Quraishawa. Shi kuma Manzon Allah (S.A.W.W) shine zababben zababbun su.

Za mu cigaba insha Allah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 31st October, 2019

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post