IDANUWA SUN YI BACCI, AMMA ZUCIYAR A FARKE TAKE !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @                     
A ko da yaushe ita zuciyar  mumini a farke take ba ta bacci kamar yadda idanuwa ke yi, amma shi fajiri da munafuki  a ko da yaushe zuciyar sa bacci take yi, shi yasa ba ta iya karbar gaskiya. Wannan dalili yasa Manzon Allah (S.A.W.W) ya misalta cewa baccin malami (mumini) ya fi ibadar jahili, domin yadda Shaidan zai iya lalata masa ibada ba zai iya rabar zuciyar mumini har yayi wani abu akan ba.

Ita kuma zuciyar Manzon Allah (S.A W W)  a farke ta ke ko da kuwa idanuwansa na bacci, sannan kuma (zuciyar sa) na karbar dukkan abinda aka zo mata da shi, ko da ace idanuwansa na bacci.

Bukhari ya riwaito cewa; Muhammad Bn Ubaadata ya bamu labari, Yazeed ya bamu labari, Saleem Bn Hayyan ya bamu labari, Sa'id Bn Meena'a ya bamu labari, ko kuma ya ji Jabir Bn Abdullahi (R.A) yana cewa;

" Mala'iku sun jewa Manzon Allah (S.A.W.W) yayin da yake bacci, sai sashen su ka ce; " BACCI FA YAKE YI." Sai wasu daga cikin su suka ce; " LALLE ITA IDANUWA TANA BACCI, AMMA ZUCIYA FA A FARKE TAKE!" Sai suka  e; " LALLE WANNAN MA'ABOCI(suka buga misali da shi), sai sashen su suka ce; " LALLESHI F A BACCI YAKE YI."

Sai sashen su suka ce; " LALLE IDANUWA TA YI BACCI, AMMA ZUCIYAR A FARKE TAKE." Sai suka ce; "

" MISALINSA (S.A.W W) KAMAR MISALIN MUTUM NE DA YA GINA GIDA KUMA YA SANYA ABINCI A CIKINSA, SANNAN YA AIKA MAI KIRA, TO, WANDA YA AMSAW MAI YIN KIRA SAI YA SHIGA GIDAN YA KUMA CI DAGA ABINCIN. WANDA DUK BAI AMSABA MAI KIRAN BA, BA ZAI SHIGA GIDAN BA KUMABA ZAI CI DAGA ABINCIN BA." Sai suka ce;

" AYI MASA WAHAYIN (a haka cikin baccin nasa) ZAI FAHINTA!" Sai wasun su suka ce; " LALLE FA BACCI YAKE YI!"

Sai sashen su suka ce;

" LALLE IDANUWA TANAA BACCI, AMMA ZUCIYAR A FARKE TAE !" Sai Zika ce;

" GIDAN SHINE ALJANNAH, MAI KIRA KUMA MUHAMMAD (S.A.W.W), DUK WANDA YA YIWA MUHAMMADU BIYAYYA, TO, ALLAHYA YIWA BIYAYYA, WANDA KUMA YA SABAWA MUHAMMAD, TO, ALLAH YA SABAWA, KUMA MUHAMMAD (S.A.W.W) SHI KE RARRABE TSAKANIN MUTANE  ".

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      08126385470

~ 12th November, 2019.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post