Sharrin dake cikin Neman Mulki..!!!

 

A BA KA BA TARE DA KA NEMA BA YA FI ALKHAIRI

Mulki wani abu ne mai girman hatsari kuma mafi sauki cikin abinda mafi yawan mutane ke so.  Da ace an san sharrin da ke cikinsa, ko kuma ba don son zuciya ba da mutum ba zai taba neman cewa a ba shi ba, amma sai kaga har kudi ake kashewa da kuma kamun qafa wajen wasu.

Abin takaici shine, ba za ka ji ana taya murna ga wanda ya nemi mulki ya rasa ba, sai dai ka ji ana taya shi baqin ciki.

Shi kuma wanda ya sami mulki maimakon a jajanta masa kan hatsarin da yake ciki, sai dai ka ji ana taya shi murna. Wani lokaci ma har daukarka a matsayin maqiye ake yi in wani ya nemi mulki ya samu ba ka fito ka taya shi murna ba.

An wayi gari yau idan ka ji ana taya mutum murna musamman ta bangaren aikin gwamnati, to, ya sami wani matsayi ne na halaka, wanda kuwa bai sami irin wannan matsayi ba, to, shi ake gani a matsayin mawahalli abin tausayi.

Ya zo cikin littafin Bukhari wanda aka fi sani da suna SAHIHI yana cewa;

Muhammad Bn Fadhl Abu  Nu'uman ya bamu labari, Jarir Bn Haazim ya bamu labari, Hassan ya bamu labari, Abdurrahman Bn Samurata ya bamu labari yace; Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" YAA ABDURRAHNAN BN SAMURATA, KADA KA ROQI SHUGABANCI, DOMIN IDAN AN BA KA ITA (shugabancin), SABODA KA ROQA, TO, SAI A BARKA DA ITA. AMMA IN BA KA (ita) AKA YI BA TARE DA KA ROQETA BA SAI A TAIMAKE KA A KANTA. IDAN KUMA KAYI RANTSUWA (kan aikata wani abu) SAI KUMA KA GA WANI ABINDA YA FI SHI ALKHAIRI, TO, KAYI KAFFARA KAN RANTSUWAR TAKA (ta hanyar fasa aikata wannan aikin da kayi rantsuwa a kansa) KA JEWA WANNAN DA YA KASANCE SHINE MAFI ALKHAIRI."

( Bukhari, hadisi na 6622).

Wannan abu ya sa ni cikin nazari na hangen wadanda ake ganinsu a matsayin malaman addini ne gaba-gaba wajen neman shugabanci ta kowacce hanya, ko kuma cusawa wasu cewa su nemi mulki.

Amma abin ban sha'awa shine, wanda ake zagi a matsayin jahili a addini da ilimin zamani KANTOMAN Qaramar hukumar Ningi, sai ya kasance mafi nisanta wajen neman shugabanci, har za ka ji yana qalubalantar masu yi masa addu'ah ta neman zarcewa. Yana cewa su bar yi masa irin wannan addu'ah, in dai su masoyansa ne to su riqa mar addu'ah kan abinda zai zame masa alkhairi a duniya da lahirarsa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~14th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post