Anci gyaran Maiyin Addu'a yayin rufe taro

ANYI RABON BABURA DON INGANTA ILIMI A QARAMAR HUKUMAR NINGI  !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AN CI GYARAN MAI YIN ADDU'AH YAYIN RUFE TARO

A yau ne laraba 13th November, 2019 aka yi rabon Babura (BOXER) guda biyar (5) a ma'aikatan ilimi ta qaramar hukumar Ningi.

Wannan rabo ko kuma kyauta ta fito ne daga hannun mai girma Gwamnan Bauchi senator Bala Abdulkadir (Qauran Bauch).

Mai girma Kantoman Ningi malam Nura 'Dan mai shari'a ne ya jagoranci raba wadannan Babura.

Cikin jawabinsa mai girma Kantoma ya gargadi wadanda su ka ci gajiyar wannan kyauta da cewa su sani lalle wadannan Babura ba an ba su don zuwa gona ko kasuwa bane, a'a, an ba su ne kawai don inganta ilimi cikin qaramar hukumar Ningi, don haka wajibi ne su lura da wadannan Babura ta hanyar ba su tsaro da kuma kula da gyaran su.

Domin bada kariya ga wadannan Babura, mai girma Kantoman Ningi ya zare zunzurutun kudi #20,000 don yi musu kwado da kuma juye.

Da aka yi masa tunatarwa kan koken Masallacin da ake ginawa a ma'aikatar sai yace duk qarshen wata a riqa zuwa wajensa ana karbar gudumawa har a cimma manufa da iznin Allah, kuma ya ce a kawo masa Motar ma'aikar wacce ta dade a kwance zai kai ta Bauchi don a gyara ta.

Malam Aliyu Adamu, library desk officer ne yayi addu'ar rufewa, sai dai da yayi addu'ah kan cewa Allah yasa Kantoma ya zama elected chairman, sai Kantoma ya ci gyaransa da cewa;

" KA CE DAI IN AKWAI ALKHAIRI GARE NI, DOMIN NI BA 'DAN MULKI DOLE BANE, ABINDA ZAI ZAMA ALKHAIRI GARE NI NE KAWAI NAKE FATA !"

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

    08126385470

 ~ 13th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post