Samari a guji yin Soyayyar Dole..!!


A koda yaushe muslimci shine jagora wajen aiwatar da dukkan abinda mutum zai yi a rayuwarsa. Wajibi ne mutum yayi dubi tare da yin nazari cikin dukkan abinda zai aiwatar yaga cewa shin hakan ya sabawa shari'a ko kuma ya zo daidai da ita?

Ba dukkan abinda bai sabawa shari'a bane yake daidai, a'a, wani lokaci yinsa ba zai haifar da alkhairi ba. Idan kuwa ya kasance haka, to  abinda yafi dacewa shine mutum ya nisanci wannan abin komai son da yake yi masa, kuma komai dadinsa.

Manzon Allah (S.A W.W) na cewa;

" IDAN 'DAYANKU YA HIMMATU DA YIN WANI ABU TO YAYI NAZARIN QAISHEN SA, IDAN YA KASANCE CIKINSA AKWAI KHAIRI DA KUMA DAIDAITO TO YA AIKATA SHI, IDAN KUMA YA KASANCE SHARRI, TO YA BAR SHI."

Sau da yawa mutum kan ga mace kuma ya nuna yana sonta, amma sai ita ta nuna ba ta sonsa. Wani mai tunani kan haqura, amma wani sai ya nace lalle sai ta aminta da shi, ko kuma ya yarda a aurar masa ita a wannan hali na qiyayya.

ILLOLIN SOYAYYAR DOLE
_________________________

Daga cikin illolinsa akwai:-

(1)- CUTARWA:- Duk matar da tace ba ta sonka kai kuma ka nace kan dole sai ta so ka, to, ka cutar da ita  domin duk abinda za kayi mata zai bata mata rai ne.

(2)- RASHIN MUTUNCI:- Ba za ka taba samun mutunci wajen matar da ka nuna dole sai ta so ka ba.

(3)- SHIGA QUNCI:- Akan sami mata masu biyayya wadanda za su iya karbar abinda ba sa so bisa dole, amma kuma sukan shiga cikin qunci sakamakon hakan.

(4)- KANGAREWA:- Wani lokaci yarinya kan iya kangara sakamakon qoqarin iyayenta kan cewa dole sai ta so abinda ba ta so.

(5)- MUTUWAR AURE:- Idan ka dauki 65% na mace-macen aure kan faru ne sanadin qiyayya.

D.S

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 9th November, 2019.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post