Mata Hudu (4) Masu Muhimmanci ga rayuwar namiji..!!


Idan ka rasa Daya (2) Daga Cikin su kayi asara..!!
Mace wata halitta ce wacce Allah ya halicce ta kuma ya daukaka darajarta tare da muhimmantar da ita ga rayuwar namiji. Kasancewarka tare da ita kan maida kai cikakken mutum mai daraja a idon duniya.

Saboda muhimmancin ta ga rayuwar dan Adam yasa Allah (T) ya samar da ita a matsayin halitta ta biyu a doron qasa, sannan kuma aka fito da ita ta hanyar haihuwa tare da namiji a haihuwar farko na 'ya'yan Adamu (A.S).

An umarce mu da girmama su tare da tausaya musu, domin su suka fi tausayawa cikin halittun 'yan Adam. Kasancewar ka tare da su na canza maka rayuwa daga halin maraici zuwa halin 'yanci da walwala.

GA MATAN NAN KAMAR HAKA
___________________________

(1)- MAHAIFIYARKA:- Ita ce wacce ta haife ka, take sonka, take kula da kai, kuma tafi kowa son ganin ka cikin farin ciki da wadata.

(2)- 'YAR'UWAR KA:- Ita ce ta kusa wajen tausaya maka kuma takan zama tamkar Uwa gare ka, yayin da wani lokaci kake zama tamkar mahaifinta.

(3)- MATAR KA:- Ita kuma abokiyar zama ce me debe maka kewa, me canza maka rayuwa tamkar kana wata duniya ba a wannan qasa Nigeria wacce ke cike da qunci da firgici ba.

(4)- 'YARKA:- Ita kuwa ta kasance sanyin idanuwa ce gare ka, kuma tamkar fulawa mai dadin kallo gare ka, wacce kallonta ke sanya maka farin ciki cikin zuciyar ka tare da bayyanarsa a fuskar ka.

IDAN KA RASA 'DAYA (1) DAGA CIKIN SU KA YI HASARA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 8th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post