Domin karfafa Soyayyar juna


Ita soyayya babu bambanci wajen nuna ta tsakanin masoya, Sarki kake ko Sheikh ko Alaramma ko kuma Ustazeey. Duk lokacin da aka furtata tsakanin juna soyayya na qara qarfafuwa.

KU RIQA KYAUTATA KALAMAI A TSAKANIN KU

Soyayya babu ruwanta da tsufa ko yarinta, duk lokacin da aka furtata sai ta girgiza zuciyar wanda aka furtawa. Abinda nake da yaqini a kansa shine, Manzon Allah (S.A.W.W) ya riqa furta kalaman soyayya ga Sayyidah Khadeejat (S.A) a halin rayuwarta da kuma yawan ambatonta bayan wafatinta.

Sannan kuma wasu sun kawo maganganu wadanda ba ni da tabbas ko yaqini a kansu cewa wai Manzon Allah (S.A W.W) ya fi son Ummul-mumina A'isha daga cikin matansa da su kayi zamani tare. Duk da cewa nasan Manzon Allah (S.A.W.W) ba zai taba bayyana cewa ya fi son wata daga cikinsu ba  kuma ba zai taba furtawa wani haka ba, amma dai dukkansu yana nuna musu soyayya a matsayin ba su haqqoqinsu kuma don muyi koyi da shi.

Imam Ja'afar (A.S) na cewa;

" KALMAR DA MUTUM ZAI FURTATA GA MATARSA CEWA; " INA SONKI, BA ZAI TABA GUSHEWA CIKIN ZUCIYARTA BA."

Saboda haka ba wai abin kunya bane ko kuma qasqanci ka kasance kana bayyana kalaman soyayya ga budurwarka ko bazawararka ko kuma matarka ba, domin hakan zai sa taji kaima sonka na qaruwa cikin birnin zuciyarta. Duk tsufar mace idan ka furta mata kalmar soyayya sai ka ga tayi maka sabon murmushi, ina kuma ga yarinya qarama?

Wannan dalili yasa nakan yawaita furtawa matata cewa; NA FI SON GANIN MURMUSHINKI FIYE DANA KOWA  !

Tare da Ado Isah Guda.

     08126385470

~ 7th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post