IMAM ALI (A.S) YA KAFA MUSU HUJJAH
Imani na amfanarwa ne Idan an dawwama cikin sa, amma canja alqawarin da aka yiwa Allah ko kuma juya baya daga umarnin Annabi (S.A.W.W) na bata ayyuka.
'Yan'uwa kada mu kasance masu cutar da kanmu ta hanyar canza koyarwar da jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) ya barmu a kai. In da za a wayi gari mu canza haqiqanin koyarwar da yayi mana, to, tabbas ayyukan mu na baya za su baci.
Kada ka zama mai shigar Bultu da sunan mai sallamawa amma kana yiwa harka illa ta hanyar zagon qasa da yin saddu ga masu qoqarin fahintar haqiqanin karantarwa Sayyid (H).
Idan ba mu manta ba bayan yiwa Abubakar mubaya'a a Saqeefah Imam Ali (A.S) ya karanto wata aya cikin Alqur'ani mai tsarki a wata rana don isar da saqo, duk da cewa wasu ba su ma fahinci abinda yake nufi ba, amma Ibn Abbas (R.A) ya fahinci akwai saqon da Imam ke son isarwa sabanin abinda suka sani na karatun ayar.
Ayar da Imam Ali (A.S) ya karanta ita ce;
" WADANDA SUKA KAFIRTA KUMA SUKA KANGE MUTANE DAGA TAFARKIN ALLAH, (Allah) YA BATA AYYUKANSU !"
(Suratul-Muhammad, aya ta 1).
Jin wannan ayar da Imam (A.S) ya kasanta sai Ibn Abbas (R.A) ya tambaye shi cewa ya karanta wannan ayar bisa wanne dalili ne?
Sai Imam (A.S) yace;
" NA KARANTA WANI ABU NE DAGA CIKIN QUR'ANI."
Sai Ibn Abbas yace eh hakane, amma ai ya karanto ne bisa wata manufa. Sai Imam (A.S) yace masa;
" BA SAN CEWA ANNABI YA HALIFANTAR DA WANE A BAYANSA BA?"
Ibn Abbas yace, eh hakane. Sai Imam (A.S) yace;
" TO, ME YASA BA KA YI MASA MUBAYA'A BA?"
Sai yace, " na ga an yi masa mubaya'a ne shine ni ma nayi."
Na taqaita maganar anan, amma dai a dau darasi cikin taqaitaccen wannan rubutu.
SABA UMARNI NA BATA AYYUKAN MUTUM KOMAI IQIRARI DA KALMAR SHAHADARSA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
~ 15th November, 2019.