Mafi yawan Musulmai ba muminai bane.!!

HALAYYARSU CE TA BAYYANA HAKA

Kamar yadda ya kasance ake gane fajiri jabberi ta hanyar halayyarsa, haka ma mumini ake gane shi. Aikin mutum da furucinsa kadai ke fassara mutum shi wanene.

Wani lokaci kuma futucin mutum na bambanta da ayyukan sa, to, shi mai wannan aiki ya tabbata cikakken munafuqi wanda qaurace masa ya zama wajibi.

Ba tare da tsawaita magana ba za muyi amfani da wani hadisi da Bukhari ya riwaito cikin wani littafinsa da ya kira shi da suna SAHIHI.

Yana cewa;

Baban Na'im ya bamu labari, Zakariya'u ya bamu labari daga Ameer yace, na ji shi yana cewa; 

" Na ji Nu'uman Bn Bashir yana cewa, Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa"

" ZA KAGA MUMINAI WAJEN JIN QAN JUNAN SU DA QAUNAR JUNAN SU DA KUMA TAUSAYIN JUNAN SU KAMAR MISALIN JIKI NE, IDAN WATA GABA (part) TA KOKA SAI SAURAN JIKIN YA 'DAU RADADI DA RASHIN BACCI  ."

(Bukhari, hadisi me lamba 6011).

Idan muka nazarci wannan hadisi za muga yana nuna mana ne cewa duk wani abinda ya sami mumini na damuwa ko tashin hankali, to, yadda ba zai iya bacci ba ko kuma yadda zai ji zogi/radadin abinda ke jikin sa haka ma dukkan mumini zai ji, kamar dai yadda mutum ke ji in Kunama ta harbi shi ko kuma yana ciwon haqori, ba wannan bangare ne kadai zai ji ba, a'a, dukkan jikin sa ne.

Amma kalli halayyar mafi yawa daga cikin musulmi kaga, damuwar kansu ce kawai ta dame su, abinda ya shafi wasu kuwa ko a jikin su.

Za ku iya gaskata ni in kun yi nazari kan halayyar da suke nunawa in an cutar da 'yan'uwa, wasu ma har murna suke yi tare da fatan Allah ya qara kan abinda ke faruwa da su, wannan kuwa ba halayyar muminai bace.

Saboda haka nace mafi yawansu ba muminai bane, kuma muslimcin su ma ba karbabbe bane. Domin da ace karbabbe ne da za su so junan su da tausayawa juna.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      08126385470

~ 1st September, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post